APC da INEC na neman kashe ni a siyasance - Okorocha

APC da INEC na neman kashe ni a siyasance - Okorocha

Biyo bayan tirka-tirka ta hana shi takardun shaidar cin zabe, cikin kalami nasa, gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya ce bala'in da ya kubutar kansa daga afkawa a jam'iyyar adawa ta PDP a halin yanzu mafi ninkuwa ya auku gare sa a jam'iyya mai ci ta APC.

A sakamakon ci gaba da haramiyar gabatar ma sa da takardun shaidar cin zabe, gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, ya yi zargin cewa jam'iyyar APC da kuma hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC sun dukufa wajen ganin bayan sa a siyasance.

Rochas Okorocha

Rochas Okorocha
Source: Getty Images

Gwamnan jihar Imo mai barin gado na ci gaba da yiwa hukumar zabe ta kasa raddi a sanadiyar rashin danka masa takardun shaidar cin zabe, biyo nasarar sa ta lashe zaben kujerar sanatan shiyyar Imo ta Yamma yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Okorocha ya zayyana hakan cikin wata hira yayin ganawa da manema labarai na jaridar The Punch cikin birnin Abuja a ranar Talatar da gabata.

KARANTA KUMA: Binciken EFCC: PDP na zargin APC da kullawa Saraki tuggu

Babu gudu babu ja da bayam gwamna Rochas ya wassafa sunayen wadanda ke da hannun cikin wannan aika-aika ta ganin bayan kudirin sa na siyasa da suka hadar da shugaban jam'iyyar na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole da kuma daya daga cikin kwamishinonin hukumar INEC, Festus Okoye.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yayin da aka shelanta nasarar gwamna Okorocha ta lashe zaben kujerar sanatan shiyyar Imo ta Arewa, sai dai babban baturen zabe Francis Ibeawuchi, ya ce ya yi shelar ne ba a son ran shi a bisa tursasawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel