Ramadan: Ba za mu amince da wa’azin batanci ba – APC ta gargadi malamai

Ramadan: Ba za mu amince da wa’azin batanci ba – APC ta gargadi malamai

Yayin da musulmai suka fara azumin watan ramadana a ranar Litinin, jam’iyyar All Progressives Congress, (APC) ta roki musulmai da su kiyayi malamai, don wannan lokacin ne ake amfani da shi wajen yada kalaman kiyayya akan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Babban sakataren sadarwa na jam’iyyar, Mallam Lanre Issa-Onilu ya bayyana gargadin a sakon watan ramadana da ya gabatar ga manema labarai.

Kakakin APC din ya shawarci yan Najeriya da su kai rahoto ga hukumomi akan masu boyewa a karkashin inuwar malamta don gudanar da mugun nufi ko neman boyan bukatunsu.

Ramadan: Ba za mu amince da wa’azin batanci ba – APC ta gargadi malamai

Ramadan: Ba za mu amince da wa’azin batanci ba – APC ta gargadi malamai
Source: Facebook

Mallam Onilu wanda ya amince a wani jawabi cewa “lamarin garkuwa da mutane, ta’addanci, rikicin kabilu da na addinai da rigingimu da sauran laifuffukan da ake daukakawa a wassu yankunan kasar sun kasance abun damuwa matuka."

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisar dattawa: Na shiga tseren ne domin nayi nasara – Ndume

Haka zalika ya yi ikirarin cewa “gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na dauke da matakai mai nau’i da dama wajen ganin ta magance rigingimu sannan ya cigaba da bayyana cewa “shugaban kasar ya bada umurni ga hukumomin tsaro masu muhimmanci da su yi maganin duk wata barazana akan harkar tsaro, su kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da ke fuskantan tashin hankali.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel