Yan bindiga sun kai farmaki gidan wani kwamishinan Nasarawa, sun kashe mutum 1

Yan bindiga sun kai farmaki gidan wani kwamishinan Nasarawa, sun kashe mutum 1

A daren jiya Litinin, wasu yan bindiga sun kai farmaki gidan kwamishinan ilimi na jihar Nasarawa, Cif Clement Uhembe sannan suka kashe dalibin ajin karshe na jami’ar tarayya da ke Lafia.

An kashe Terlumum Hemba da misalin karfe 1:00 na tsakar dare a gidan kwamishinan da ke yankin Kaduna Koro na Lafia hanyar Lafia-Makurdi.

Wani idon shaida, wanda ya bayyana sunansa a matsayin Daddy, yace yaana labe a cikin wata mota a harabar gidan lokacin da yan bindigan suka iso gidan kwamishinan.

Yace yan bindigan sun duba harabar gidan, sannan suka fatattaki Hemba inda suka yi ta dukansa da sanduna har sai da ya mutu malemale cikin jini.

Yan bindiga sun kai farmaki gidan wani kwamishinan Nasarawa, sun kashe mutum 1

Yan bindiga sun kai farmaki gidan wani kwamishinan Nasarawa, sun kashe mutum 1
Source: UGC

An tattaro cewa kwamishinan ya yi tafiya zuwa Port Harcourt tare da wasu daga cikin iyalansa domin halartan bikin dansa lokacin da lamarin ya afku.

Idon shaidan yace maharani sun yi amfani da wukake da adda wajen shiga gidan.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisar dattawa: Na shiga tseren ne domin nayi nasara – Ndume

DPO da ke kula da sashin Agyragu, Mista Biam, ya tabbatar da lamarin, cewa ana gudanar da bincike.

Yace an kai gawar marigayin zuwa asibitin kwararru na Dalharu Araf.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa rundunar yan sanda a jihar Kano ta kama wasu Mutum uku, wadanda ake zargi da birge wani Abdulaziz Lawan, mai shekara 23 na yankin Fagge Quarters a Kano da mota sannan suka daba masa wuka har lahira.

DSP Abdullahi Haruna, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Kano, wanda ya bayyana hakan a wani jawabi a ranar Litinin, ya bayyana cewa masu laifin sun yi amfani da mota kirar Mercedes Benz 180 C-Class wajen aikata laifin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel