Kungiyar Kwadago ta Kasa ta Gargadi Ajimobi da Makinde da Su Bar sa Siyasa a Kaddamar da Albashi Mafikaranci a Jihar Oyo

Kungiyar Kwadago ta Kasa ta Gargadi Ajimobi da Makinde da Su Bar sa Siyasa a Kaddamar da Albashi Mafikaranci a Jihar Oyo

- Kungiyar Kwadago ta Kasa ta gargadi Ajimobi da Makinde da su bar sa siyasa a kaddamar da mafikarancin albashi a jihar Oyo

- Abun takaici ne gwamna mai jiran gado da mai barin gado a jihar su sa siyasa cikin al’amarin jin dadin ma’aikatan jihar

Kungiyar Kwadago (NLC) sashen jihar Oyo ta gargadi gwamnan jihar mai barin gado Senator Abiola Ajimobi da mai jiran gado Injiniya Seyi Makinde da su dakatar da wasan kwaikwaiyon siyasar da su ke yi cikin al’amarin kaddamar da albashi mafi karanci na N30,000 a jihar wanda gwamnatin tarayya ta aminta da shi.

A cikin wani bayanin da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun magatakardanta Kwamred Ibrahim Mohammed, tayi gargadin cewa abunda mutanen ke yi ya isa don kungiyar ba za ta aminta da duk wani uzurin da gwamnan mai jiran gado da mai barin gado zasu bayar ba game da kaddamar da mafi karancin albashi da tuni Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar kaddamar da shi.

Kamar yadda kungiyar ta fada, abun takaici ne gwamna mai jiran gado da mai barin gado a jihar su sa siyasa cikin al’amarin jin dadin ma’aikatan jihar.

“Wannan abu bai muna dadi ba ko kadan, kuma ya tilasta mu mu bayyana rashin jin dadin mu kan yadda ake sa siyasa a cikin al’amarin mafi karancin albashi

KU KARANTA: Gwamna Ganduje Yace Zai Ma Hukumar Hizbah Gyaran Fuska

“Kuma kungiyar kadago na kan bakanta cewa ba za ta aminta da kowane irin uzuri ba daga gwamnonin” In ji kungiyar ta NLC.

Kungiyar na bukatar zama da mukarraban gwamnatin jihar kan sha’anin albashi da giratutin da ake bin gwamnati bashi, da wasu hakkokin da ma’aikata ke bin gwamnati.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel