Shugabancin majalisar dattawa: Na shiga tseren ne domin nayi nasara – Ndume

Shugabancin majalisar dattawa: Na shiga tseren ne domin nayi nasara – Ndume

Tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Ali Ndume, ya nuna karfin gwiwar cewa zai zamo Shugaban majalisar dattawa ta tara, a wata mai zuwa.

Koda dai jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta nuna Sanata Ahmad Lawan ne zabinta a wannan kujera, Ndume ya dogara da goyon bayan takwarorinsa da shugabannin jam’iyyar.

Da yake jawabi ga manema labarai a Lagas, a jiya Litinin, 6 ga watan Mayu, Ndume, wanda yace bai shiga tseren domin yin cinikin kowani mukami mai gwabi-gwabi ba, ya jadadda cewa ya tuntubi Shugaban kasa Muhammadu Buhari, babban jigon APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu da sauran shugabannin jam’iyya mai mulki, akan kudirisa, sannan kuma cewa dukkansu sun sanya masa albarka a kudirinsa.

Shugabancin majalisar dattawa: Na shiga tseren ne domin nayi nasara – Ndume

Shugabancin majalisar dattawa: Na shiga tseren ne domin nayi nasara – Ndume
Source: UGC

Ndume ya ci gaba da bayyana cewa, babu wanda ya nemi ya janye ma wani daga tseren.

Tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisan yace hatta da Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, yayi bayanin cewa jam’iyyar dai ta gabatar da Sanata Lawan ne a matsayin dan takarar da tafi so sannan ba wai tana kokarin tursasa shi akan sanatoci bane.

Da yake Magana akan ajandarsa, Ndume wanda a yanzu yake wakiltan Borno ta kudu, yayi alkawarin inganta kokarin da majalisa ta takwas tayi, sannan ya kara da cewa zai rage kwadaitar da mukamin Shugaban majalisar dattawa ga mutane ta hanyar rage wasu abubuwa marasa amfani da ke jingine da kujerar.

KU KARANTA KUMA: A wata mai tsarki: Yan sanda sun kama mutum 3 kan zargin kashe wani matashi a Kano

Yayinda yake alkawarin ba bangaren dokoki yancinsu, sanatan yayi alkawarin aiki tare da bangaren zartarwa ba tare da la’akari da banbancin iko ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel