Babban Bankin Najeriya ya fara binciken asusun ajiyar masu fasa kaurin kayayyakin sawa

Babban Bankin Najeriya ya fara binciken asusun ajiyar masu fasa kaurin kayayyakin sawa

- Babban Bankin Najeriya Ya Fara Binciken Asusun Ajiyar Masu Fasakaurin Kayan Da Ake Yi da Auduga

- Manufar shirin shine farfado da darajar audugar Najeriya da sha’anin saka dadunke-dunke.” In ji shugaban bankin

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Mr. Godwin Emefiele yace a halin yanzu bankin ya fara binciken asusun ajiyar kamfanoni da mutanen dake da hannu cikin fasakaurin kayan da ake sakawa da auduga zuwa kasar nan.

Mr Emefiele ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da rabon irin auduga da wasu kayan aiki ga manoman auduga sama da dubu dari a jihar Katsina don noman damanar shekarar 2019.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje Yace Zai Ma Hukumar Hizbah Gyaran Fuska

Manufar shirin shine farfado da darajar audugar Najeriya da sha’anin saka dadunke-dunke.”

Bukata ita ce tantance kamfanoni da mutanen dake da hannu cikin gurbatattar sana’ar

“Za a hana duk bankunan Najeriya harkokin ciniki da kamfanonin, da masu su da kuma jami’an dake gudanar da su. Yin haka zai taimaka wurin inganta noman auduga daga ton 80,000 da aka noma a cikin shekarar 2018 zuwa ton 300,000 a shekara 2020." In ji shugaban bankin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel