A wata mai tsarki: Yan sanda sun kama mutum 3 kan zargin kashe wani matashi a Kano

A wata mai tsarki: Yan sanda sun kama mutum 3 kan zargin kashe wani matashi a Kano

- Jami'an yan sandan jihar Kano sun kama wasu mutum uku a kan laifin halaka wani matasi

- Masu lafin sun bige matashin da mota sannan suka soke shi har lahira

- Yan sanda na ci gaba da bincike sannan za a tura su kotu da zaran an kammala

Rundunar yan sanda a jihar Kano ta kama wasu Mutum uku, wadanda ake zargi da birge wani Abdulaziz Lawan, mai shekara 23 na yankin Fagge Quarters a Kano da mota sannan suka daba masa wuka har lahira.

DSP Abdullahi Haruna, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Kano, wanda ya bayyana hakan a wani jawabi a ranar Litinin, ya bayyana cewa masu laifin sun yi amfani da mota kirar Mercedes Benz 180 C-Class wajen aikata laifin.

Haruna ya bayyana cewa lamarin ya afku ne a ranar 6 ga watan Mayu, da misalin karfe 3:00 na rana.

A wata mai tsarki: Yan sanda sun kama mutum 3 kan zargin kashe wani matashi a Kano

A wata mai tsarki: Yan sanda sun kama mutum 3 kan zargin kashe wani matashi a Kano
Source: Depositphotos

Kakakin yan sandan ya ci gaba da zargin cewa an kama masu laifin a lokacin da suke kokarin yasar da gawar mamacin a Abedi hanyar France Sabon Gari Quarters.

A cewarsa, an gano motar da suka yi amfani da ita a matsayin hujja.

KU KARANTA KUMA: Badakalar bindiga da kudi: Ganduje ya sake farfado da binciken Sarkin Kano

Ya bayyana cewa anyi gaggawan daukar marigayin zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad Kano, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Haruna yace rundunar ta fara bincike akan lamarin, sannan kuma cewa zata tura masu laifin kotu bayan bincike.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel