Kotu ta Daure Masu Hannu a Magudin Jarabawar ta 2019

Kotu ta Daure Masu Hannu a Magudin Jarabawar ta 2019

- Kotu ta Daure Masu Hannu a Magudin Jarabawar ta 2019

- An gurfanar da mutane 123 a gaban kuliya don fuskantar shari’a kan aikata laifukka daban-daban da suka shafi magudin jarabawa

Shugaban Hukumar JAMB mai shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare UTME, Prof Ishaq Oloyede yace kotu ta daure mutane biyar da aka samu da hannu dumu-dumu a magudin jarabawar da aka yi ta 2019, na tsawon watanni ukku zuwa shekaru biyu, kuma yanzu haka an gurfanar da mutane 123 a kotunan dake fadin kasar nan kan zargin da ake masu na hannu a cikin magudin.

A wata takardar labarai da hukumar ta JAMB ta samar tace “mutane ukku daga jihar Zamfara da wasu biyu daga jihar Kebbi kotu ta daure su na tsawon watanni ukku zuwa shekaru biyu.

KU KARANTA: Hukumar Jarabawar JAMB ta fara tantance bayanan dalibbai sama da miliyan 1 da suka zauna jarabawa

An gurfanar da mutane 123 a gaban kuliya don fuskantar shari’a kan aikata laifukka daban-daban da suka shafi magudin jarabawa, kuma hukumar ta roki sashen shari’a da ya cigaba da irin wannan aikin don tabbatar da an hukunta duk wadanda ake zargi kuma aka samu cikakkiyar shaida kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel