Ba sani ba sabo: Rundunar Yansanda ta bayyan dalilinta na cafke Sanatan PDP

Ba sani ba sabo: Rundunar Yansanda ta bayyan dalilinta na cafke Sanatan PDP

Rundunar Yansandan Najeriya ta bayyana dalilin da yasa ta kama Sanatan jam’iyyar PDP dake wakiltar mazabar Osun ta yamma, kuma tsohon dan takarar gwamnan jahar Osun, Sanata Ademola Adeleke.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar, Frank Mba ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, inda yace sun kama Sanata Adeleke ne saboda bincikensa da suke yi da hannu cikin tafka mummunan laifi.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Gwamnan Kano ya fara kulle kullen tsige Sarkin Kano

Ba sani ba sabo: Rundunar Yansanda ta bayyan dalilinta na cafke Sanatan PDP

Adeleke
Source: Twitter

Da fari dai rundunar ce ta fara aika ma Sanatan wasikar gayyata zuwa babban ofishinta dake babban birnin tarayya Abuja, amma isarsa keda wuya sai jami’an rundunar suka garkameshi, suka hanashi tafiya.

“A yanzu haka Sanata Adeleke na hannunmu, da yammacin 6 ga watan Mayu muka kamashi, kuma kamen nasa yana da nasaba da zarginsa da ake yi da hannu cikin tafka babban laifi, tuni muka bashi takardun dake kunshe da zarge zargen da muke masa, kuma zamu mikashi gaban kotu a ranar Talata 7 ga watan Mayu.” Inji Frank.

Majiyarmu ta ruwaito rundunar Yansanda na tuhumar Sanata Adeleke ne da aikata laifin satar amsa a yayin daya zana jarabawar kammala makarantar sakandari, wanda hakan babban laifi ne a kundin dokokin Najeriya.

Sai dai kwamitin yakin neman zaben Sanata ta zargi jam’iyya mai mulki ta APC da hannu cikin kama Sanatan,inda ta bayyana lamarin a matsayin wata bita da kulli. Ita ma jam’iyyar PDP ta nemi Yansanda suyi gaggawar sako Sanata Adeleke.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel