Jami’an tsaro sun sabawa doka wajen kama Sanatan Osun Adeleke – PDP

Jami’an tsaro sun sabawa doka wajen kama Sanatan Osun Adeleke – PDP

Mun samu labari cewa jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya, tayi kira ga jami’an ‘yan sandan kasar nan da su saki Sanata Ademola Adeleke wanda ta kama kwanan nan, ba tare da wani bata lokaci ba.

PDP tayi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja bayan da Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Mista Kola Ologbondiyan, ya kira wani taro na gaggawa da manema labarai a jiya Ranar Litinin 6 ga Watan Mayun nan.

Kola Ologbondiyan yayi Allah-wadai da matakin da gwamnatin APC mai mulki ta dauka na damke ‘Dan takarar gwamnan na jihar Osun. Ologbondiyan yake cewa cafke Ademola Adeleke da aka yi ya sabawa ka’ida da dokokin Najeriya.

KU KARANTA: Kotun Tarayya ta aikawa Shugaban kasa sammaci

Jami’an tsaro sun sabawa doka wajen kama Sanatan Osun Adeleke – PDP
Sanata Ademola Adeleke yayi nasara a kan APC a zaben Osun
Asali: Twitter

Jam’iyyar hanayyar take cewa gwamnatin Buhari ta sa an kama ‘dan takarar gwamnan ne saboda a kawo cikas wajen sauraran karar zaben da ake yi tsakanin ‘dan takarar na PDP da kuma gwamnan Osun mai-ci Gboyega Oyetola.

PDP tace kwanan nan Alkalin wani babban Kotu da ke Osun ya bada hukuncin da ya hana ayi ram da Ademola Adeleke da mukarraban sa. Duk da wannan umarni jami’an tsaro sun yi gaba sun kama Sanatan a farkon makon nan.

Kotu tace ka da wanda ya taba Ademola Adeleke har sai zuwa lokacin da aka kammala binciken da ake yi a game da zargin satifiket PDP tace Sanatan na ta, mutum ne mai bin doka don haka babu dalilin a kama shi har a garkame.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel