Wata sabuwa: Gwamnan Kano ya fara kulle kullen tsige Sarkin Kano

Wata sabuwa: Gwamnan Kano ya fara kulle kullen tsige Sarkin Kano

Dangantaka tayi tsami yayin da gwamnan jahar Kano,Abdullahi Umar Ganduje ya fara shiri tare da kulle kullen tsige mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yanzu haka gwamnan ya fara amfani da hukumar karbar koke koke da yaki da rashawa ta jahar Kano wajen sake farfado da binciken masarautar da ta fara yi tun kimanin shekaru biyu da suka gabata inda ake zargin Sarki da facaka da kudin masarautar.

KU KARANTA: Ka yi mun gani: El-Rufai ya bayyana yadda za’a karya siyasar uban gida a jahar Legas

Wata sabuwa: Gwamnan Kano ya fara kulle kullen tsige Sarkin Kano

Wata sabuwa: Gwamnan Kano ya fara kulle kullen tsige Sarkin Kano
Source: UGC

Haka zalika majalisar dokokin jahar ta fara tattauna batun kirkirar wasu sabbin masarautu masu cin gashin kansu guda hudu a jahar Kano, Bichi, Gaya, Karaye da Rano, kamar yadda kaakakin majalisar, Kabiru Alhassan Rurum ya karanta wasikar wani mai suna Ibrahim Salisu daya bukaci haka.

Sai dai wani maijiya daga fadar gwamnatin Kano ya shaida ma majiyarmu cewa “Gwamnan ya dage kai da fata sai tsige Sarki, amma idan kuma bai samu nasara ba, zai raba masarautar don ya rage masa karsashi.”

Wannan mataki da Ganduje ke shirin dauka yayi daidai da matakin da surukinsa, gwamnan jahar Ogun, Abiola Ajimobi ya dauka wajen rage ma Sarkin Ibadan, Olubadan karfin iko ta hanyar nada sabbin sarakuna guda 21.

Wannan jikakkiyar rikici dake tsakanin Gwamna Ganduje da Sarkin Kano ta faro ne tun daga lokacin da Sarkin ya taba sukar gwamnan game da yawan yawace yawacen da yake yi zuwa kasashen turai, da kuma sukar da yayi game da kwangiyar aikin jirgin kasa da gwamnan ya baiwa wata kamfanin China.

Jim kadan bayan wannan magana ne hukumar yaki da rashawa ta jahar Kano ta kaddamar da bincike kan zargin Sarkin da kashe naira biliyan shida ba tare da samun izinin gwamna ba. Koda yake wani marubuci Jaafar Jaafar neya fara bayyana badakalar kashe kashen kudi a fadar Sarki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel