Badakalar bindiga da kudi: Ganduje ya sake farfado da binciken Sarkin Kano

Badakalar bindiga da kudi: Ganduje ya sake farfado da binciken Sarkin Kano

Hukumar yaki da rashawa da karbar koke koke ta jahar Kano ta sake farfado da binciken data fara yi akan mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II game da zargin da take yi masa na bindiga da kudaden asusun masarautar Kano.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kimanin shekaru biyu da suka gabata ne dai hukumar ta fara kaddamar da wannan bincike, amma daga bisani ta dakatar dashi bayan majalisar dokokin jahar Kano ta dakatar da nata binciken a ranar 22 ga watan Mayun 2017, kamar yadda Ganduje ya bukata.

KU KARANTA: Ka yi mun gani: El-Rufai ya bayyana yadda za’a karya siyasar uban gida a jahar Legas

Badakalar bindiga da kudi: Ganduje ya sake farfado da binciken Sarkin Kano

Badakalar bindiga da kudi: Ganduje ya sake farfado da binciken Sarkin Kano
Source: UGC

Sai dai wata wasika da hukumar ta aika ma sakataren masarautar dake dauke da kwanan wata 2 ga watan Mayu ta umarci wasu manyan jami’an fadan Sarki guda hudu dasu bayyana a gabanta don amsa wasu tambayoyi game da kudaden da masarautar ta kashe daga shekarar 2013 zuwa 2017.

Wadannan manyan jami’ai da hukumar ta gayyata sun hada da shugaban ma’aikatan mai martaba Sarki, Mannir Sunusi, sakataren Sarki, Mijitaba Abubakar, babban akantan fada, Mohammad Kwaru da tsohon sakataren sarkin, Isa Sunusi.

Hukumar ta kara da cewa tana da hurumin gayyatar jami’an fadan kamar yadda sashi na 9 dana 15 na kundin dokokinta ya bata damar binciken duk wani kokari na yi ma sashi na 26 karan tsaye, sashin daya shafi kula da kudaden da ake kashewa a majalisar Sarki.

A wani labari kuma, a kokarinsa na karya lagon mai martaba Sarkin Kano, gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nemi sahhalewar majalisar dokokin jahar don kirkirar sabbin masarautu masu zaman kansu guda hudu, Karaye, Bichi, Rano da Gaya.

Duk kudurin dokar kafa masarautun ba daga gwamnan ta fito ba, dan majalisa Ibrahim Salisu ne ya bayyana kudurin a gaban majalisar, amma ana zargin gwamnan nada hannu cikin kokarin rage ma Sarki masarautarsa sakamakon zargin da yake yi masa na goyon bayan Abba Gida Gida a zaben gwamnan Kano.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel