Hukumar kula da gidajen yari ta kori babban Ofisa saboda safarar kwayoyi

Hukumar kula da gidajen yari ta kori babban Ofisa saboda safarar kwayoyi

Shugaban hukumar kula da gidajen yari na kasa (NPS), Ja'afaru Ahmed, ya amince da shawarar kwamitin ladabtarwa na shiyyar 'C' a kan korar wani babban ma'aikacin hukumar mai suna Umar Adamu bayan samun sa da laifin safarar miyagun kwayoyi zuwa cikin gidan yari.

Kakakin hukumar NPS na kasa, DCP Francis Enobore, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Litinin.

Ya ce matakin da shugaban ya dauka na daga cikin kokarin hukumar gidajen yari na tabbatar da da'a da kuma tsare fursunoni daga samun miyagun kwayoyi.

"Ko ba a fada ba, kowa ya san cewar shigar da kwaya gidajen yari ya saba da manufar gidajen yari na gyara halayen fursononi da kuma tsare lafiyar su," a cewar kakakin.

Hukumar kula da gidajen yari ta kori babban Ofisa saboda safarar kwayoyi
Shugaban hukumar kula da gidajen yari; Ahmed Jafaru
Source: Twitter

Shugaban gidajen yarin ya gargadi jami'an hukumar a kan cin amana da saba dokar aiki, ya bayyana cewar hukumar ba za tayi jinkirin sallamar duk jami'in da ta samu da aikata laifi ba.

DUBA WANNAN: Fatima Bala, makahuwa 'yar baiwa, ta samu tallafi daga gidauniyar kasar Qatar

Ya bayar da tabbacin cewar hukumar NPS ba zata bari wasu jami'anta su lalata zaman lafiyar da ta samar a gidajen yarin dake fadin kasar nan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel