'Yan sanda sun tsare sanatan PDP Ademola Adeleke a Abuja

'Yan sanda sun tsare sanatan PDP Ademola Adeleke a Abuja

Rundunar 'yan sanda a Abuja ta tsare Sanata Ademola Adeleke, dan takarar PDP da ya sha kaye a zaben gwamnan jihar Osun, bayan ya masa gayyatar da suka yi masa a ranar Litinin.

Adeleke, Sanata mai wakiltar jihar Osun ta yamma a majalisar dattijai, ya kai kan sa hedikwatar 'yan sanda dake Abuja amma hakan bai hana su tsare shi ba.

Wata kotun tarayya dake Abuja ta bawa Sanata Adeleke izinin yin bulaguro zuwa kasar Amurka domin a duba lafiyar sa. Ranar Talata, 7 ga watan Mayu ne ranar da zai tashi zuwa kasar Amurka.

Alkalin kotun, jastis Inyang Ekwo, ne ya umarci sanatan da ya amsa gayyatar rundunar 'ya sanda kafin ya fita daga Najeriya. Amma sai ga shi rundunar 'yan sandan ta tsare shi bayan ya bi umarnin kotun.

'Yan sanda sun tsare sanatan PDP Ademola Adeleke a Abuja
Sanata Ademola Adeleke
Source: Depositphotos

Tuni jam'iyyar PDP tayi korafi a kan kama tare da tsare dan takarar ta a zaben gwamnan jihar Osun da aka yi a shekarar 2018.

Jam'iyyar ta ce tsare sanata Adeleke ya nuna cewar rundunar yan sandan ta nuna raini ga hurumin kotu.

DUBA WANNAN: Fatima Bala, makahuwa 'yar baiwa, ta samu tallafi daga gidauniyar kasar Qatar

Duk da rundunar 'yan sanda ba ta fito ta bayyana dalilin tsare Adeleke ba, makusantan shi na zargin cewar ba zai rasa nasaba da batun gurfanar da shi da rundunar tayi a kan zarginsa da yin cuwa-cuwar takardar kammala sakandre ta WAEC ba.

Rundunar 'yan sanda ta fara kama Adeleke a watan Satumba na shekarar 2018 bisa zarginsa da gabatar da sakamakon jarrabawar WAEC mai cike da alammomin tambaya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel