Fatima Bala, makahuwa 'yar baiwa, ta samu tallafi daga gidauniyar kasar Qatar

Fatima Bala, makahuwa 'yar baiwa, ta samu tallafi daga gidauniyar kasar Qatar

Wata matsiyar makahuwa mai suna Fatima Bala, wacce ta karanta ayoyin Al-qur'ani yayin rabon kyautar wasu Al-qur'anai na zamani guda 100 a jihar Sokoto, ta samu ta samu tallafin karatu daga wata gidauniyar jin kai ta kasar Qatar.

Fatima ta makance shekaru 6 da suka wuce a wani yanayi mai matukar daure kai.

Da take magana da wakilin jaridar Daily Trust, Fatima ta ce burinta a rayuwa shine ta zama likita, amma saboda kaddarar da ta same ta, yanzu ta canja ra'ayinta na son zama likita zuwa karatun yaren Arabic ko Turanci a kwalejin ilimi dake Sokoto.

"Ba zan iya jure karatu a muhallin jami'a ba saboda yanayin da na tsinci kai na. Ba iya makanta ce matsala ta ba, ina da matsalar ciwon kafa ma, wacce ba ta iya bari nayi tafiya mai tsawo kuma ga shi akwai nisa tsakanin dakin kwanan dalibai zuwa ajuzuwan daukan darasi," a cewar matashiyar.

Fatima Bala, makahuwa 'yar baiwa, ta samu tallafi daga gidauniyar kasar Qatar

Sultan Sa'ad Abubakar III
Source: Depositphotos

Sannan ta cigaba da cewa, "na dade ina burin samun tallafin da zai bani damar cigaba da karatu na, saboda shine burina tun bayan kammala karatuna na sakandire."

DUBA WANNAN: An samu gawar wata budurwa da ta fara rubewa a dakin kwanan daliban jami'ar Jos

Da yake magana da manema labarai, babban sakataren kungiyar gidauniyar ta kasar Qatar a Najeriya, Dakta Hamdi Muhammad, ya ce zasu dauki karatun matashiyar a duk makarantar da ta samu gurbin karatu a Najeriya.

A cewar sa, gidauniyar su tafi kauri a wajen bayar da tallafi a harkar ilimi, musamman ga mutane masu rauni ko bukata ta musamman.

Ya ce gidauniyar na bayar da tallafin 10,000 ga marayu dubu a jihohn Najeriya 15 baya ga gina makarantu, Masallatai da haka rijiyoyi domin amfanin jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel