Kotu ta aikewa da Buhari sammaci a kan tsohon Alkalin Alkalai na Najeriya, Onnoghen

Kotu ta aikewa da Buhari sammaci a kan tsohon Alkalin Alkalai na Najeriya, Onnoghen

Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a garin Abuja, ta aikewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari sammaci tare da mukaddashin alkalin alkalai na Najeriya, Tanko Muhammad domin bayyana mata dalilai na tsige tsohon alkalin alkalin na kasa, Mai Shari'a Walter Onnoghen.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kotun tarayya ta aikewa da shugaban kasa Buhari sammaci da dukkanin sauran masu ruwa domin bayyana ma ta dalilai na tsige tsohon alkalin alkalai na kasa daga mukamin sa na jagorancin hukumar shari'a ta kasar nan.

Buhari tare da Onnoghen
Buhari tare da Onnoghen
Source: Twitter

Alkalin kotun Mai Shari'a Inyang Ekwo, ya bayar da umurni na neman dukkanin mambobin cibiyar shari'a ta tarayya, gwamnatin tarayya, lauyan kolu na kasa da kuma majalisar dattawa akan bayyana dalilai da zai dakile haramcin tabbatar da Mai Shari'a Tanko Muhammad a matsayin sabon alkalin alkalai na kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa, lauya mai kare hakkin dan Adam, Malcolm Omirhobo, shi ne ya shigar da wannan korafi na neman kotu ta haramtawa shugaban kasa Buhari tabbatar da Mai Shari'a Tanko Muhammad a matsayin alkalin alkalai na kasar nan.

KARANTA KUMA: Bayan shekaru 16, EFCC ta fara bincike a kan gwamnatin Saraki

Lauya Malcolm na neman kotun ta gudanar da bincike domin tabbatar da an kiyaye duk wani tanadi da doka da kundin tsarin mulkin kasa ya gindaya wajen tsige Mai Shari'a Onnoghen tare da maye gurbin sa da Mai Shari'a Tanko a ranar 25 ga watan Janairun 2019.

Bayan da hukumomi masu ruwa da tsaki wajen hana yiwa tattalin arziki ta'annati suka kammala bincike, a ranar Alhamis 18 ga watan Afrilun 2019, kotun kiyaye da'a ta kasa ta cimma matsaya wajen tabbatar da zargi na laifin rashin bayyana kadarorin da Mai Shari'a Onnoghen ya mallaka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel