Siyasar Kano: Majalisa na so a tsaga Masarautar Kasar Kano

Siyasar Kano: Majalisa na so a tsaga Masarautar Kasar Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta fara shirin yin gutsun-gutsun da Masarautar kasar zuwa gidaje 4. Yanzu haka ana so a kirkiri wasu sababbin Sarakuna a Yankin Gaya, Karaye, Bichi da kuma kasar Rano.

Wani ‘dan majalisa, Salisu Ibrahim Chambers, shi ne ya fara kawo wannan kudiri a gaban zauren majalisar inda yake neman sauran Abokan aikinsa su amince da hakan. Wannan kudiri ya jawo ce-ce-ku-cen gaske a zaman da aka yi.

Dole dai majalisar ta dakatar da zaman zuwa lokaci na gaba bayan ganin ‘yan majalisar jihar sun gaza cin ma matsaya inda wasu ke nuna goyon bayan su a kan wannan magana, yayin da wasu ‘yan majalisar su ka tubure su kace a’a.

Wadannan sababbin Sarakuna da ake so a nada a kasar Gaya, Karaye, Bichi da Rano, za su sa yawan Sarakunan jihar Kano su zama 5. Kowane Sarki zai samu mukamin Sarki mai iko mai matakin farko a kasar ne idan hakan ta tabbata.

KU KARANTA: Ganduje zai gyarawa Hukumar Hizbah zama a Kano

Siyasar Kano: Majalisa na so a tsaga Masarautar Kasar Kano

Rikicin Sarki da Gwamna ya sa za a tsaga Masarautu a Kano
Source: UGC

Masana harkar siyasa sun ce wannan shiri da majalisar dokokin ta kawo, bai rasa nasaba da rikicin da ake yi tsakanin gwamnatin jihar Kano da kuma Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II wanda ake ganin bai tare da gwamnati.

Tsohon Kakakin majalisar Kano, Alhaji Isiyaku Ali Danja, ya nuna rashin amincewar sa da wannan kudiri inda yayi kira ga sauran ‘yan majalisa su guji taba gidan Sarautar. Wannan ya sa majalisa ta bada lokaci domin a sake duba lamarin.

Sai dai manyan ‘Yan APC a majalisa irin su Alhaji Baffa Babba Danagundi sun goyi bayan kudirin. Baffa Babba Danagundi yace a dokar kasa, majalisar jihar tana da hurumin tsage masarautar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel