Bayan shekaru 16, EFCC ta fara bincike a kan gwamnatin Saraki

Bayan shekaru 16, EFCC ta fara bincike a kan gwamnatin Saraki

Hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, ta bayyana rahoton cewa, ta fara gudanar da bincike kan shugaban majalisar dattawa na Najeriya Abubakar Bukola Saraki tun daga lokacin da ya kasance gwamnan jihar Kwara a shekarar 2003 kawowa yanzu.

A yayin rashin fayyace daliln fara gudanar da bincike kan tsohon gwamnan na jihar Kwara, hukumar EFCC cikin sakon da ta wassafa a shafin ta na dandalin sada zumunta ta bayyana cewa, binciken ba ya da wata alaka da sabon nadin mukamin Saraki a matsayin jakadan cibiyar kare hakkin dan Adam ta kasa-da-kasa.

Bayan shekaru 16, EFCC ta fara bincike a kan gwamnatin Saraki

Bayan shekaru 16, EFCC ta fara bincike a kan gwamnatin Saraki
Source: Depositphotos

Tuni dai hukumar mai hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta aike da sakon neman izinin duk wasu takardu da shaidu dangane kudaden da Saraki ya samu yayin rike akalar jagoranci ta gwamnatin jihar Kwara a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011.

Majiyar jaridara Legit.ng ta ruwaito cewa, tun a shekarar 2016 kawowa yanzu, ana ci gaba da takun saka tsakanin Saraki da hukumar EFCC biyo bayan hawa kujerar naki ta majalisar dattawa akan rashin amincewa da nadin Ibrahim Magu a matsayin jagoran hukumar.

KARANTA KUMA: Jam'iyyu 75 sun amince da sakamakon zaben shugaban kasa na 2019

Cikin wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, bayan shekaru 9 da rasuwa, a jiya Lahadi 5, ga watan Mayun 2019, Saraki ya yi alhinin tunawa da mutuwar tsohon shugaban kasa, Marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar Adu'a.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel