Sace surukin Buhari ya nuna cewa ba a ba Daura kula na musamman – Fadar Shugaban kasa

Sace surukin Buhari ya nuna cewa ba a ba Daura kula na musamman – Fadar Shugaban kasa

Babban mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a fannin sadarwa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa sace Hakimin Daura, Alhaji Musa Uba, wanda ya ke siriki ga babban dogarin shugaba Buhari, ya nuna cewa jami'an tsaron kasar nan ba sa nuna son kai wurin tabbatar da tsaro a jihohi da garuruwan kasar nan.

Haka kuma, kwamishinan 'yan sandan jihar ta Katsina, Sanusi Buba, ya koma garin Daura a karshen makon nan domin mayar da hankali wurin ceto Hakimin.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da aka yi wata hira da shi a gidan talabijin na AIT.

Da yake amsa tambayoyi game da cigaba da ake samu na matsalar garkuwa da mutane a kasar nan, ganin yadda aka sace Hakimi dungurum daga mahaifar shugaban kasa, Shehu ya ce, "Kwarai hakan ya faru, amma hakan ya na nuni da cewa matsalar masu garkuwa da mutanen ta shafi kowanne lungu da sako na kasar nan, kuma saboda shugaban kasa ya fito daga garin Daura hakan ba yana nufin cewa ba ayin laifi a Daura ba.

Sace surukin Buhari ya nuna cewa ba a ba Daura kula na musamman – Fadar Shugaban kasa

Sace surukin Buhari ya nuna cewa ba a ba Daura kula na musamman – Fadar Shugaban kasa
Source: Twitter

"Kwana biyu da suka gabata hukumar soji ta bayyana cewa, akwai alamun cewa matsalar tsaro a kasar nan ta wuce iya ta 'yan ta'adda kawai."

Bayan haka kuma da aka tambaye shi kan ya zai bayyana gwamnatin shugaba Buhari a fannin yaki da ta'addanci, Shehu ya ce, "Zai bai wa gwamnatin maki 98 a cikin dari a fannin yaki da ta'addanci."

KU KARANTA KUMA: Najeriya na bukatar tsayayyen jagora kamar Shugaban kasa Buhari – Babban malami

Hakazalika da ya ke mayar da martani akan bayanin, shugaban hukumar 'yan sanda na kasa, Mohammed Adamu, inda ya bayyana cewa mutane 1,071 ne suka rasa rayukan su a farkon shekarar nan ta 2019, Shehu ya ce, duk da irin matsalar da ake samu ta 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane a wannan gwamnatin, kashe-kashen bai kai na gwamnatin da ta gabata ba.

Ya kuma kare shugaban kasar akan tafiyar da ya yi kasar Birtaniya na tsawon kwanaki 11 duk da matsalar tsaron da ake fama da shi a kasar.

Ya bayyana cewa shugaban kasar na da damar hutawa, kuma duk da haka ya na kula da duk abubuwan da suke faruwa a kasar lokacin da ya ke birnin Landan din.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce jami'an tsaron kasar nan suna yin iya bakin kokarin su, kuma ya kamata mutane su san cewa ba a kawo canji a lokaci daya, dole sai an bi komai a hankali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel