'Yan bindiga sun sace mutum biyu a harin da suka kai gidajen malaman kwalejin kimiyya a Filato

'Yan bindiga sun sace mutum biyu a harin da suka kai gidajen malaman kwalejin kimiyya a Filato

Wasu 'yan bindiga da ba sa san ko su waye ba sun kai hari gidajen malaman kwalejin kimiyya a Heipang, karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato, tare da yin awon gaba da 'yar uwar mataimakin rajistaran makarantar, Ezekiel Rangs.

Lamarin na zuwa ne watanni uku bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari gidajen malaman tare da sace dan babban limamin cocin makarantar, Rabaran Andrew Dido, kafin daga baya su sako shi bayan biyan kudin fansa.

Wata jami'ar 'yar sanda da ta nemi a boye sunanta ta tabbatar wa da jaridar SaharaReporters kai harin, ta ce 'yan bindigar sun dira a rukunin gidajen malaman tsakar dare, lokacin da kowa ke bacci, tare da yin awon gaba da karamar kanwar rajistaran makarantar, Ezekiel Rangs.

"Sun yi amfani da dutse wajen balle kofar dakin matashiyar, wacce aka sanar da mmu cewar ba ta dade da samun gurbin karatu a makarantar ba," a cewar 'yar sandan.

Ta cigaba da cewa; "sannan sun yi awon gaba da wayar hannu ta wani dake gidan, alamar da ta nuna cewar zasu tuntubi 'yan uwanta domin neman kudin fansa."

Kazalika, wani dalibi ya tabbatar da cewar 'yan bindigar sun sace matar wani malami da ya zuwa yanzu ba gano waye malamin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel