Rayuwarmu na cikin hatsari don mun mara wa Buhari baya – Uwargidar Obasanjo ta koka

Rayuwarmu na cikin hatsari don mun mara wa Buhari baya – Uwargidar Obasanjo ta koka

- Taiwo Obasanjo ta koka kan zargin barazana ga rayuwarta

- Uwargidar tsohon Shugaban kasar tace ana farautar rayuwarta ne saboda goyon bayan shugaba Buhari da tayi

- Tayi ikirarin cewa ta samu bayanai abun dogaro kan yunkurin kashe ta

Uwargidar tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Misis Taiwo Obasanjo, ta bayyana cewa rayuwarta da ta danta Olujonwo na cikin barazana saboda hukuncinsu na mara wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a zaben da ya gabata.

Da take hira da jaridar Vanguard a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu, Uwargidar Obasanjo tace an sanar da ita cewa wani da bai ji dadin hukuncinta na mara wa Buhari baya ba, ya tura makasa domin su kashe ta da danta wanda ya mara wa shugaba Buhari baya a bainar jama’a.

Misis Obasanjo tace makasan na son fara kashe ta sannan su mayar da abun kamar aikin fashi da makami.

Rayuwarmu na cikin hatsari don mun mara wa Buhari baya – Uwargidar Obasanjo ta koka

Rayuwarmu na cikin hatsari don mun mara wa Buhari baya – Uwargidar Obasanjo ta koka
Source: UGC

A cewarta bayan nan sai su dawo su kashe danta, Olujonwo a wani harin na fashi da makami.

“Tun lokaci da ni da dana muka nuna goyon bayanmu ga gwamnatin Buhari da kudirinsa na neman tazarce, Baba Obasanjo bai yi farin ciki damu ba. Ina rokon duk wanda ya san ‘Baba’ da yayi hakuri ya fada masa cewa kada ya kashe ni da dana. Kada ya zama laifi da zai yi sanadiyar mutuwata da dana saboda mun mara wa Buhari baya.

KU KARANTA KUMA: Najeriya na bukatar tsayayyen jagora kamar Shugaban kasa Buhari – Babban malami

“Ina kuma rokon hukumar yan sanda da sauran hukumomin tsaro da suyi hakuri su kawo mana agaji. Wannan babban barazana ne don haka yan sanda su taimaka mana. Wannan ba wai wani yunkuri na janyo hankalin mutane bane,” inji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel