Najeriya na bukatar tsayayyen jagora kamar Shugaban kasa Buhari – Babban malami

Najeriya na bukatar tsayayyen jagora kamar Shugaban kasa Buhari – Babban malami

Ubaka Ifeanbunike, babban limamin cocin St. Peter’s Church, Enugwu –Ukwu, yace Najeriya na bukatar tsayayyen jagora kamar Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin magance matsalolin da kasar ke fuskanta.

Ifeabunike ya fadi hakan ne a lokacin fatawarsa a ranar Lahadi a cocin St Peter’s Church Enugwu-Ukwu da ke karamar hukumar Njikoka na jihar Anambra.

Yace akwai bukaatar al’umman Najeriya su jajirce domin su habbaka tattalin arziki da ma’aikatun kasar.

Yace yan Najeriya sun ki mayar da hankali ka-in da na-in wajen ayyukansu daban-daban.

Najeriya na bukatar tsayayyen jagora kamar Shugaban kasa Buhari – Babban malami

Najeriya na bukatar tsayayyen jagora kamar Shugaban kasa Buhari – Babban malami
Source: Twitter

“Amma duk da haka suna son zama masu arziki a dare daya ba tare da bin tsaunin rayuwa ba.

“Aiwatar da abunda ya rataya a wuyarsu na yin abunda ya kamata a lokacin da ya kamata, sannan cewaa hakan yasa mutane da yin abunda bai da amfani wanda ba zai kari kasar da komai ba,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi wa inna illaihi raji’un: Magaji Ubandoman Gombe ya rasu yana da shekara 80 a duniya

Yace shugaba dake da dakewar zuciya da mayar da hanakali ga manufofi kamar Buhari zai gyara matsalolin tattain arziki da sauransu wanda kasar ke fuskanta.

Yace ya kamata yan Najeriya su koyi yin abunda ya kamata a lokacin da ya kamata ba tare da sun jira wani ya lura da su ba sannan ya bukaci da su ajiye lalaci sannan su rungumi kwazon aiki wanda zai kai ga ci gaba da habbaka tattalin arzikin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel