Bahallatsar alkalin Alkalain: Masu kokarin kawo ma Buhari tasgaro sun ji kunya a gaban kotu

Bahallatsar alkalin Alkalain: Masu kokarin kawo ma Buhari tasgaro sun ji kunya a gaban kotu

Wasu gungun lauyoyi dake kalubalantar mukaddashin Alkalin Alkalai, Tanko Muhammad tare da kokarin ganin sun yi amfani da kotu wajen haramta ma shugaban kasa Muhammadu Buhari nada Tanko a matsayin Alkalin Alkalai mai cikakken iko sun ji kunya a gaban kotu.

Tun a watan Janairun shekarar 2019 ne Muhammad yake rike da mukamin riko na Alkalin Alkalai bayan shugaba Buhari ya fatattaki tsohon Alkalin Alkalai Walter Onnoghen wanda daga bisani yayi murabus bayan an kamashi da laifin rashawa, hakan tasa ake tsimayin Buhari ya rantsar da Muhammad.

KU KARANTA: Muhimman fa’idojin watan Ramadan guda 11 daya kamata Musulmi ya sani

Bahallatsar alkalin Alkalain: Masu kokarin kawo ma Buhari tasgaro sun ji kunya a gaban kotu

Muhammad Tanko
Source: UGC

Sai dai Legit.ng ta ruwaito wasu gungun lauyoyi a karkashin jagorancin Lauya Malcom Omirhobo sun shigar da kara gaban wata babbar kotun tarayya suna kalubalantar cancantar Muhammad na zama Alkalin Alkalai.

Amma da yake shari’a sabanin hankali ne, sai Alkalin kotun, mai sharia Inyang Ekwo yayi watsi da bukatar lauyan na haramta ma Buhari rantsar da Muhammad Tanko a matsayin sabon Alkalin Alkalai mai cikakken iko.

A ranar Juma’a, 3 ga watan Mayu ne Alkali Inyang ya yanke wannan hukunci, inda yace ba zai amsa bukatun masu kara ba, sai dai su fara zuwa su sanar da wadanda suke kara karar da suka shigar dasu a gaban wannan kotu.

Sa’annan yace da zarar masu kara sun sanar da wadanda suke kara game da karar da suka shigar dasu, shi kuma ya baiwa wadanda ake kara kwanaki 7 dasu gurfana a gabansa don kare kansu daga bukatar masu kara, sa’annan ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Mayu.

Wadanda aka shigar da karan sun hada da majalisar shari ta koli, hukumar kula da ma’aikatan sharia, Alkalin Alkalai na riko, gwamnatin tarayya, shugaba Buhari, Ministan sharia da kuma majalisar dokokin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel