Mutane 41 sun hallaka a gobarar jirgin sama

Mutane 41 sun hallaka a gobarar jirgin sama

- Wani hatsarin jirgin sama a filin jirgin sama na Moscow yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 41

- Jirgin saman na kasar Rasha yayi saukar gaggawa bayan ya kama da wuta

- Wasu daga cikin fasinjojin da suka tsira sun fita ne ta kofar agajin gaggawa na daya gefen jirgin

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa akalla fasinjoji 41, ciki arda yara biyu ne suka rasa ransu bayan wani jirgin saman Rasha ya yi hatsari a filin jirgin sama na Moscow a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu.

Jirgin saman na Aeroflot SU 1492 yayi saukar gaggawa sannan kuma ya kama da wuta a filin jirgin saman Sheremetyevo da ke birnin Moscow, CNN ta ruwaito.

A take sai wasu daga cikin fasinjojin jirgin suka fita ta kofar agajin gaggawa na daya gefen jirgin domin kubutar da rayuwarsu.

Wani bidiyo mai cike da alhini ya nuna yadda jirgin yayi saukar gaggawa da gudu kafin ya daki kasa, inda hakan yasa ya kara bin iska sannan ya sake dukan kasa inda hakan yasa shi kamawa da wuta.

Akwai mutane 78 a cikin jirgin wanda ya hada da ma’aikatan jirgi biyar, inda daga cikinsu mutane 37 sun tsira, biyar na samun kulawar likitoci a yanzu haka, Elena Markovskaya, mai Magana da yawun kwamitin binciken Rasha ta tabbatar.

KU KARANTA KUMA: Anyi ta kokarin lasa mun zuma don na murde zaben Kwara na 2019 - Kwamishinan zabe

Wasu sun zargi fasinjoji da rashin imani wajen ceto yan uwansu fasinjoji yayinda suka sukufa wajen ceto jakunkunansu maimakon ceto sauran mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel