Majalisar dokokin jihar Kano ta fara yunkurin kirkirar karin masarautu 4

Majalisar dokokin jihar Kano ta fara yunkurin kirkirar karin masarautu 4

Majaliar dokokin jihar Kano ta fara yunkurin kirkirar karin wasu masarautu hudu a jihar Kano mai yawan kananan hukumomi 44.

Yayin zaman majalisar na ranar Litinin, kakakin majalisar, Alhaji Alhassan Rurum, ya karanta wasikar da Ibrahim Salisu da wasu mutane suka kawo dake neman majalisar ta fara yunkurin kirkirar karin wasu masarautu hudu a jihar.

Karaye, Bichi, Rano da Gaya ne sabbin masarautun hudu da ake saka ran majalisar za ta kirkira.

Majalisar ba ta bayyana yaushe za ta kada kuri'ar neman amincewar mambobinta a kan wannan kudiri ba.

Majalisar dokokin jihar Kano ta fara yunkurin kirkirar karin masarautu 4

Majalisar dokokin jihar Kano
Source: UGC

Sai dai, ta kafa kwamitin da zai kawo mata rahoto a kan kudirin, ana saka ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa a gaban majalisar a ranar Talata, 7 ga watan Mayu.

DUBA WANNAN: Dawowar buhari: Fadar shugaban kasa ta gwasale 'yan adawa da kafafen yada labarai

Masu neman a kara kirkirar masarautun, sun bayyana cewar su na son majalisar tayi dokar da za ta daidaita darajar sarakunan ta zama daya da ta sarkin Kano.

Batun kirkirar karin sarakunan yanka hudu ba zai yiwa masarautar Kano dadi ba, wacce ta dade ta na mulkin masarauta ma fi girma da fadi a arewacin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel