Dalilin da yasa Zamfara ke bukatar N10bn domin sake gina ta – Marafa

Dalilin da yasa Zamfara ke bukatar N10bn domin sake gina ta – Marafa

Sanata Kabiru Garba Marafa ya bayyana cewa jihar Zamfara na bukatar naira biliyan 10 da aka amince mata a matsayin kasafin kudin 2019 saboda irin kangin rayuwar da mutanenta suka shiga tsawon sekaru da dama sanadiyar ayyukan yan bindiga.

Marafa wanda ke jagorantar kwamitin majalisar dattawa kan man fetur, yayi godiya ga abokan aikinsa a majalisun dokokin kasar biyu kan samar da adadin kudin, wanda aka yiwa lakabi da tallafi na musamman domin sake gina jihar Zamfara.

Dan majalisan a ranar 10 ga watan Afrilu ya gabatar da korafi kan lamarin inda ya koka akan ci gaban ayyukan yan fashi a jihar Zamfara, wanda ya sanya rayuwar mutane a cikin kangi sannan ya mayar da dubban mutane suka zama marasa galihu.

Dalilin da yasa Zamfara ke bukatar N10bn domin sake gina ta – Marafa

Dalilin da yasa Zamfara ke bukatar N10bn domin sake gina ta – Marafa
Source: Depositphotos

A wani jawabi dauke da sa hannunsa a jiya Lahadi, Marafa, wanda ke wakiltan Zamfara ta tsakiya, yace tarin goyon bayan da takwarorinsa daga majalisun dokokin kasar biyu ke bayarwa ya nuna cewa da hadin kai da alkiblar da suka fuskanta, kasar za ta shawo kan matsalolinta.

KU KARANTA KUMA: Buhari yayi jawabin farko yayinda ya isa Abuja daga Landan

Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kafa kwamitin wucin gadi wanda za a nada ma suna shirin tallafin Shugaban kasa kan jihar Zamfara wato PIZAMS, da wa’adin shekaru 10 sannan ya roki Shugaban kasar da yayi gaggawan kafa PIZAMS kamar yadda yake a shirin maajalisar dattawa.

Yace abun bakin ciki ne shekaru takwas da aka kwashe cikin duhun ayyukan yan bindiga, daga 2011 har yau, a jihar Zamfara hakan yayi sanadiyar kashe samada da maza manya 11,000, inda hakan yayi sanadiyar mayar da mata 22,000 zawaea da kuma marayu akalla 44,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel