Anyi ta kokarin lasa mun zuma don na murde zaben Kwara na 2019 - Kwamishinan zabe

Anyi ta kokarin lasa mun zuma don na murde zaben Kwara na 2019 - Kwamishinan zabe

Malam Garba Madami, kwamishinan zabe na jihar Kwara a ranar Litinin, 6 ga watan Mayu ya bayyana cewa yaki amsar kudi da yan siyasa suka basa domin ya keta haddin zaben 2019 da aka gudanar a jihar.

Madami wanda ya fito daga karamar hukumar Gurara da ke jihar Niger ya bayyana hakan ga manema labarai bayan bikin yarsa a Minna.

“Na fuskanci matsin lamba daga yan siyasa wadanda suka yi kokarin bani kudi don na yi magudi a zaben 2019 da ya gudana a jihar Kwara amma na tsaya akan kafafuna sannan naki bayar da kai bori ya hau.

“Yanayin aikinmu a hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) yana da kwadaitarwa sosai.

“Ya rage tsakaninka da Allanka yin abunda ya kamata sannan ka tsira da mutuncinka ko kuma ka bayar da hadin kai mutuncinka ya zube. Kana iya tafiya gidan yari,”.inji shi.

Anyi ta kokarin lasa mun zuma don na murde zaben Kwara na 2019 - Kwamishinan zabe

Anyi ta kokarin lasa mun zuma don na murde zaben Kwara na 2019 - Kwamishinan zabe
Source: Original

Ya kuma koka kan suyasar kudi da kuma lamari inda yan siyasa ke ganin za su iya siyan mutuncin mutum don kazamin aikinsu.

“Yan siyasa na da kudi sannan wasun su na ganin za su iya siyan kowa da kudi.

“Ana maganar mutunci ne, ya rage gare ka kayi taka-tsantsan sannan kayi aiki da gaskiya don tsira da mutuncinka.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisa: Dattawan Arewa maso gabas sun amince da kudirin Ndume

“Abunda nayi a jihar Kwara kafin zabe shine na fito na sanar da mutane cewa babu yawan kudin da zai iya siya na

“Na fahimtar dasu cewa kuri’unsu zai yi tasiri sannan ban shirya yin magudi ba,” inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel