Ziyarar da na kai birnin Landan ba ta da alaka da nadin Ministocin Majalisa ta - Buhari

Ziyarar da na kai birnin Landan ba ta da alaka da nadin Ministocin Majalisa ta - Buhari

A ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya dawo Najeriya daga tafiyar sa bayan shafe tsawon kwanaki goma wajen ziyarar da ya kai birnin Landan na kasar Birtaniya.

Sabanin rade-radi na rahotanni, shugaban kasa Buhari ya ce tafiyar sa ba ta da wata alaka ta kusa ko ta nesa da harkallar nadin Ministocin da za su yi riko na wasu madafan iko a sabuwar gwamnatin sa cikin wa'adin ta na biyu.

Buhari yayin dawowar sa daga birnin Landan

Buhari yayin dawowar sa daga birnin Landan
Source: Twitter

Shugaban kasa Buhari kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi cikin babban birnin kasar nan na tarayya bayan dawowar sa daga ziyarar kwanaki goma da ya kai birnin Landan.

Domin kawar da shakku, shugaban kasa Buhari ya ce tafiyar sa ba ta da wata nasaba da nadin Ministocin sabuwar gwamnatin sa. Ya ce babu karo ko guda da ya tattauna da wani mahaluki a kan nadin Ministocin sa yayin ziyarar sa a birnin Landan.

KARANTA KUMA: Ina taya Musulman Najeriya murnar shigowar watan Azumi - Buhari

Dangane da sauya shiri da kuma taku na tunkarar ta'addanci a fadin kasar nan, shugaban kasa Buhari ya ce ya yi amanna da kwazon mukaddashin sufeto janar na 'yan sanda, Muhammad Adamu, wajen fafutikar sa ta kawo karshen wannan mummunar annoba da ta zamto alakakai a Najeriya.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin tuntuba ta manema labarai, shugaban kasa Buhari ya hau kujearar ta yin tsokaci ko kuma wani karin haske dangane da yadda sabuwar majalisar sa za ta kasance.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel