Ina taya Musulman Najeriya murnar shigowar watan Azumi - Buhari

Ina taya Musulman Najeriya murnar shigowar watan Azumi - Buhari

A ranar Litinin, 1 ga watan Ramalana na shekarar 1445 bayan hijirar fiyayyen halitta, Manzon tsira daga birnin Makka zuwa Madina, wanda ya yi daidai da 6 ga watan Mayun 2019, daukacin al'ummar Musulmi sun tashi da azumi a fadin duniya.

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya aike da sakon sa na taya murna ga daukacin al'ummar Najeriya musamman Musulman da ke cikin kasar a yayin da aka fara gudanar da daya daga cikin mafificiyar ibada ta azumin Ramalana.

Mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu, yayin wata sanarwa da ya gabatar a ranar Lahadin da ta gabata cikin garin Abuja, ya ce shugaban kasa Buhari ya na miko gaisuwar sa ga daukacin al'ummar Najeriya biyo bayan bayyanar sabon jaririn watan Azumi a bana.

Ina taya Musulman Najeriya murnar shigowar watan Azumi - Buhari
Ina taya Musulman Najeriya murnar shigowar watan Azumi - Buhari
Source: Facebook

Shugaban kasa Buhari kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, ya yi kira na neman al'ummar Najeriya da su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da kuma aminci a fadin kasar.

A cewar shugaban kasa Buhari, Musulunci ya kasance mafificin addini da ya zamto babban ginshiki na zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da shimfidar koyarwa ta akidu masu kawar da kiyayya a tsakanin al'umma.

KARANTA KUMA: Watan Azumin Ramalana ya bayyana a Najeriya - Sarkin Musulmi

Buhari ya yi kira na neman al'ummar Musulumi da su ribaci tabarraki na lokutan azumi wajen kulla kyakkyawar alaka da kwanciyar hankali da hadin kai a tsakanin su da mabiya sauran addinai.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya mika kokon barar sa wajen kwarara addu'o'i na neman Mai Duka ya dawwamar da zaman lafiya, ci gaba da kuma aminci a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel