Ramadan: Saraki ya bukaci Musulmai da su roki zaman lafiya da tsaro

Ramadan: Saraki ya bukaci Musulmai da su roki zaman lafiya da tsaro

- Bukola Saraki, yayi kira ga Musulmi da su roki ci gaban Najeriya

- Saraki yace azumin Ramadan na nuni ga tsarki zuciya da kuma sabonta imani

- A cewar Shugaban majalisar dattawa, kasar zata iya amfana sosai daga addu’o’in masu imani a wannan lokaci

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki yayi kira ga Musulmai da su yi addu’a domin ci gaban Najeriya yayinda suka bi sahun takwarorinsu na duniya wajen fara azumin Ramadan.

Saraki a wani sakon fatan alkhairi a Abuja a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu, domin shiga wata mai tsarki, ya bayyana cewa tunda azumi na nuni ga tsarkin zuciya da sabonta imani, kasar na iya amfana daga addu’o’in masu takawa a wannan lokacin.

Ramadan: Saraki ya bukaci Musulmai da su roki zaman lafiya, tsaro da ci gaban tattalin arziki
Ramadan: Saraki ya bukaci Musulmai da su roki zaman lafiya, tsaro da ci gaban tattalin arziki
Source: Twitter

Saraki ya kuma yi kira ga shugabanni da su samar da manufofi da shirye-shirye da zai amfani jama’a da kuma matasa a kasar.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisa: Ba zan yi jayayya da yancin yan majalisa ba – Ndume

Ya kara da cewa hauhawan matasa a kasar albarka ne yayinda matasa ka iya karfafa tsare-tsaren ci gaba cikin sauri.

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II yayi kira ga kafatanin al’ummar Musulmai dasu jajirce wajen gudanar da addui’o’i a wannan wata mai alfarma na watan Azumin Ramadana domin kawo karshen matsalar tsaro a yankin Arewacin Najeriya.

Sarki Sunusi ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu a yayin taron daura auren mata 70 da gwamnatin jahar Kano ta dauki nauyinsu, inda yace ya kamata Musulmai su dage wajen yin addu’o’i ko Allah zai dubemu da idon rahama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel