Shugabancin majalisa: Dattawan Arewa maso gabas sun amince da kudirin Ndume

Shugabancin majalisa: Dattawan Arewa maso gabas sun amince da kudirin Ndume

- Kudirin takarar Sanata Ali Ndume na neman shugabancin majalisar dattawa na kara samun karfi

-Tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan ya samu yardarm kungiyar dattawa da masu ruwa da tsaki a arewa maso gabas

- Kungiyar ta kuma yi kuma yi Allah wadai da yunkurin tursasa wa yan majalisar shugabanni da wasu mutane a jam’iyyar APC ke yi

Takarar Sanata Ali Ndume na neman shugabancin majalisar dattawa na tara, a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu ya samun yardae dattawa da masu ruwa da tsaki a yankin arewa maso gabas.

Da suke lamuncewa Ndume, kungiyar sun bayyana cewa takardunsa sun fi na dukkanin mutanen da ke neman kujerar.

Shugabancin majalisa: Dattawan Arewa maso gabas sun amince da kudirin Ndume

Shugabancin majalisa: Dattawan Arewa maso gabas sun amince da kudirin Ndume
Source: Facebook

Sun kuma yi Allah wadai da yunkurin tursasa wa yan majalisar shugabanni da wasu mutane a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yunkurin yi.

KU KARANTA KUMA: Buhari yayi jawabin farko yayinda ya isa Abuja daga Landan

Dattawan sunce sun yanke shawarar mara mara wa Ndume baya ne bayan sun auna cancantar sauran yan takaran inda suka ga cewa shine mafi cancanta a cikinsu.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Sanata mai wakiltan yankin Borno ta kudu a majalisar dokokin kasar, Mohammed Ali Ndume, ya bayyana cewa ba zai yi jayayya da yancin majalisar dattawa ba idan aka zabe shi a matsayin Shugaban majalisar a yayin rantsar da majalisa ta tara.

Ndume yace yana son jagorantar majalisar dattawa ta tara ne, domin ya taimaka waje ganin majalisar dokokin kasar tayi shugabanci naari, inda ya kara da cewa majalisar na bukatar tsayayyen mutum daga yankin arewa maso gabas da zai jagorance ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel