Hukumar Jarabawar JAMB ta fara tantance bayanan dalibbai sama da miliyan 1 da suka zauna jarabawa

Hukumar Jarabawar JAMB ta fara tantance bayanan dalibbai sama da miliyan 1 da suka zauna jarabawa

- Hukumar jarabawar JAMB ta fara tantance bayanan yatsun dalibai da Miliyan daya da dubu dari takwas

- Dalibai da dama da suka rubuta jarabawar ta UTME sun roki hukumar da ta fitar da sakamakonsu.

Hukumamar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare (JAMB) ta fara tantance bayanan yatsun dalibai miliyan daya da dubu dari takwas wadanda suka zauna hadaddiyar jarabawar neman shiga makarantun gaba da sakandare (UTME).

Rahotanni sun bayyana cewa aikin tantance bayanan da hukumar ta fara ne ya kawo tsaikon fitar da sakamakon jarabawar wadda aka gudanar daga 11 zuwa 18 ga watan Afirilu.

Tuni dai hukumar ta gudanar da tantance bayanan dalibbai a jihohi 31. Yanzu haka tana kan tantance bayanan dalibbai a sauran jihohi shidda na kasar nan, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje zai ma Hukumar Hizbah Gyarn Fuska

Magatakardar hukumar ta JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede, ya tabbatar da hakan ga wakilin jaridar ta The Nation a Abuja.

Yace hukumar na binciken kome wanda ya shafi yadda jarabawar ta gudana, wanda ya hada da bayanan yatsun dalibai.

Da aka tambaye shi lokacin da hukumar za ta saki sakamakon jarabawar ta UTME, magatakardar yace bai sani ba, amma yana kyautata zaton nan ba da dadewa ba, da zarar sun kammala aikin da suke yi.

Magatakardan ya karyata cewar da ake yi wai hukumar za ta soke rabin sakamakon jarabawar wasu jihohin da aka samu da magudi a lokacin jarabawar.

Da aka tambaye shi wace jiha ce tafi matsalar magudin jarabawar, sai yace shi bai sani ba.

Oloyede yace babu wata matsalar da ta shafi kundin adana bayanan hukumar na yanar gizo, sai dai hukumar na kokarin kauda bara gurbi ne daga cikin tsarin ilimi.

Magatakardan hukumar yace: "za a binciki zargin da ake yi wa wasu ma’aikatan hukumar wadanda suka hada baki da wasu cibiyoyin gudanar da jarabawar da ake rubutawa da na’ura mai aiki da kwakwalwa (computer based test centre operators) don aikata magudin jarabawa".

."Za gudanar da bincike a duk wuraren da aka samu wani ma’aikaci da hannu a cikin danyen aikin. Ya kara da cewa duk inda aka samu wani ma’aikacin hukumar na din-din-din ko na wucin gadi da hannu cikin aikata abunda bai kamata ba za a dauki matakin da ya dace." In ji Magatardan'

A halin yanzu dalibai da dama da suka rubuta jarabawar ta UTME sun roki hukumar da ta fitar da sakamakonsu. Amma hukumar tace za ta gudanar da aikin tantancewar cikin tsanaki saboda ta gano cewa an aikata abubuwan da ba dai-dai ba masu yawa a lokacin gudanar da jarabawar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu. Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel