Zaben 2019: Kotu za ta saurari korafin Atiku a cikin makon nan

Zaben 2019: Kotu za ta saurari korafin Atiku a cikin makon nan

Mun fahimci cewa kotun da ke sauraron karar zaben shugaban kasa da aka yi a Najeriya, zai sa lokaci domin somin-tabin sauraron hujjojin korafin da ‘dan takarar PDP, Atiku Abubakar, ya kawo.

Jaridar Punch tace akwai yiwuwar kotu ta saurari korafin da Lauyoyin Alhaji Atiku Abubakar su ke yi game da zaben 2019 ya gabata a cikin wannan makon da aka shiga. Jaridar ta Punch ta rahoto wannan ne a Ranar Litinin 6 ga Watan Mayu.

Watakila a cikin makon nan ne kotun da ke sauraron karar zaben zai zauna domin shiryawa sauraron duk dalilai na karar da Lauyoyin Atiku Abubakar su ka kawo. A tsarin kotun, za ta karkare wannan zaman sauraron karan ne a cikin makonni 2 rak.

Bayan an gama wannan zama, kotu za ta sa rana domin cigaba da ainihin shari’ar da ake yi. Dokar kasa ta ba wannan kotu na musamman damar kammala shari’ar ta ne a cikin kwanaki 180. Manyan Alkalai 5 ne za su yanke hukunci a karshe.

KU KARANTA: Atiku ba 'Dan Najeriya bane - APC ta bayyanawa kotu

Atiku Abubakar wanda yake ikirarin shi ne ya lashe zabe, ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, ya sanar da kotu cewa yana da tarin hujjoji da kuma shaidu akalla 400 da za su yi jawabi domin nunawa Duniya gaskiyarsa a gaban kuliya.

Punch tace kawo yanzu Atiku ya nemi kotu ta fara shirin sauraron korafin da yake da su bayan ya sanar da wadanda yake tuhuma game da zaman shari’ar. Za a fara sauraron hujjoji ne bayan mako guda da tuntubar wadanda ake kara.

Manyan Lauyoyin da su ka tsayawa jam’iyyar PDP sun bayyanawa manema labarai cewa su na jira ne kurum a sa ranar da za a fara sauraron karar a kotu. Lauyoyin APC a na su bangaren sun tabbatar da wannan inda su ka fara shirin kare kan-su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel