Shugaba Buhari bai da karfin kula da Najeriya, inji Afegbua

Shugaba Buhari bai da karfin kula da Najeriya, inji Afegbua

Kakakin PDP, Mista Kassim Afegbua, wanda ya kasance bako a shirin talbijin din Channels a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu yace Shugaban kasar bai da karfin jagorantar Najeriya wajen fita daga rikiccin tsaro da take ciki.

Afegbua ya kuma zargi gwamnatin tarayya da kin magance rashin tsaro, inda yayi ikirarin cewa zai kasance abun mamaki idan har kanun labarai bai kasance dauke da kowani rahoton kisa ba.

Kalamunsa: “Shugaban kasar bai da karfin kula damu saboda yana nan yana ji da kansa ne.

“Ina ganin abuna muka fuskanta a shekaru hudu da suka gabata maimaicu ne na irin rikon sakainar kashin da ake wa lamarin tsaro a kasar nan.

Shugaba Buhari bai da karfin kula da Najeriya, inji Afegbua

Shugaba Buhari bai da karfin kula da Najeriya, inji Afegbua
Source: Twitter

“Kada ku manta kundin tsarin mulki (kamar yadda aka gyara a 1999) ya bayyana karara abu na farko da ya rataya akan wuyan gwamnati, musamman gwamnati da ta yi wa sunata da gwamnati mai yakar cin hanci da rashawa da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

“Kuma kamar yadda muke Magana a yau, ba tare da jayayya ba, za ku yarda dani cewa abun mamaki ne idan kanen labaran gobe bai kasance sayke da kashe-kashe ba saboda kusan kullun idan ka karanta jarida yana dauke da kashe-kashe da dama."

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisa: Ba zan yi jayayya da yancin yan majalisa ba – Ndume

Da yake martani ga zargin, Adesina yace matsalolin tsaro ya batun yau bane, dadadde lamari ne kamar Najeriya.

Sannan kuma ya jadadda jajircewar Shugaban kasar wajen magance matsalar tsaro yadda ya kamata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel