Falana ya so na Najeriya ta rika aiki da hukuncin Kotun Nahiyar Afrika

Falana ya so na Najeriya ta rika aiki da hukuncin Kotun Nahiyar Afrika

Femi Falana, wanda babban Lauya ne mai kare hakkin Bil Adama, ya shigar da kara a gaban kotun tarayya da ke zama a Abuja da nufin cewa gwamnatin Najeriya ta rika yi wa kotun Nahiya biyayya.

Punch ta rahoto cewa Femi Falana SAN ya roki babban kotun tarayya da ke Abuja da ta umarci gwamnatin tarayyar Najeriya ta san da zaman kotun Nahiyar Afrika, kuma ta yi biyayya ga duk hukuncin da ta ke yankewa ‘yan kasar.

Falana a karar da ya shigar mai lamba ta FHC/ABJ/CS/356/2019, ya bayyana cewa Najeriya tana cikin kasashen da ba su aiki da abin da Kotun Nahiyar Afrika da ke Tanzaniya ta fada, yana mai neman Najeriya ta rika yi wa Kotun biyayya.

A halin yanzu Najeriya tana cikin kasashen Afrika 30 na kungiyar AU ta Nahiyar, kuma tana cikin wadanda ke da wakili a kotun Afrikan, sai dai kasar ba ta yarda da karfin wannan kotu ba don haka Falana yake neman a sake duban wannan lamari.

KU KARANTA: Buhari ya dawo Najeriya bayan ya shafe kwanaki a Ingila

Falana ya so na Najeriya ta rika aiki da Kotun Nahiyar Afrika

Femi Falana yace Najeriya tana sabawa wasu dokokin Nahiyar Afrika
Source: Depositphotos

Lauyan yana so a ba ‘yan kasar Najeriya damar zuwa gaban irin wannan kotu da ke kasar Tanzaniya su kai kukansu har kuma a saurari korafin, a yanke hukuncin da ya dace. Hakan na nufin sai an yi wa wani bangare na dokar kasar nan kwaskwarima.

Kasashen AU 9 ne rak su ke aiki da matakin da wannan Kotu na Nahiyar ta yanke. Wannan kasashe su ne: Algeria, Benin, Burkina Faso, Cote D’voire, Ghana, Gambiya, Mali, Malawi, da ita kan ta kasar Tanzaniya da a nan wannan Kotu ta ke aiki.

Tun a 2011 Najeriya ta ke cewa za ta rika bin umarnin wannan Kotu amma har yau ba ta cika wannan alkawari ba. Yanzu dai Femi Falana ya nemi Ministan shari’ar Najeriya ya amince da karfin kotun Nahiyar domin ‘Yan Najeriya su rika kai kara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel