NYSC ta bayyana abinda yasa Boko Haram suka yi awon gaba da matashi dan bautan kasa

NYSC ta bayyana abinda yasa Boko Haram suka yi awon gaba da matashi dan bautan kasa

Hukumar kula da matasa masu yima kasa hidima ta NYSC tayi karin haske game da matashin dan bautan kasa da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram tayi garkuwa dashi a garin Chibok, Abraham Amuta, inda tace matashin bai nemi izininta ba wajen zuwa garin ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu ne yan Boko Haram suka yi awon gaba da Amuta tare da wani Faston cocin Living Faith Church Worldwide, Oyeleke a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Chibok don kai ma jama’an garin kayan agaji.

KU KARANTA: Wata sabuwa: An dakatar da sana’ar Acaba a wasu manyan jahohin Arewa guda 5

NYSC ta bayyana abinda yasa Boko Haram suka yi awon gaba da matashi dan bautan kasa

Amuta
Source: UGC

Kaakakin NYSC reshen jahar Borno, Muhammad Sada yace Amuta yayi gaban kansa ne zuwa garin Chibok ba tare da neman izinin hukumar ba, ya kara da cewa sai ta hanyar cocin ne ma suka samu labarin satar matashin da Boko Haram tayi.

“Cocin sun aiko mana a rubuce cewa mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da wani dan bautan kasa na rukunin B, inda suka ce cocin ta aiki Fasto Oyeleke ne zuwa garin Chibok domin kai ma yan gudun hijira kayan tallafi.

“Cocin ta fada mana cewa Amuta baya cikin wadanda zasu kai wannan kayan agaji, amma ya dage kai da fata cewa lallai sai ya bisu zuwa garin Chibok, don haka ya tafi zuwa Chibok a karkashin kulawar cocin ba tare da neman izinin NYSC ko sanar damu ba.

“Kamar yadda kowa ya sani, muna baiwa yan bautan kasa damar sauya jaha sakamakon matsalar tsaron da ake fama dashi a Borno, haka zalika bama tura wani dan bautan kasa zuwa duk inda muka san rayuwarsa zata shiga cikin hadari.” Inji shi.

Daga karshe Muhammad yace tuni sun sanar da dakarun Soji halin da Amuta yake ciki, don daukan matakin daya dace.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel