Tabarbarewar tsaro a Arewa: Sarkin Kano ya bayyana matakin daya dace Musulmai su dauka

Tabarbarewar tsaro a Arewa: Sarkin Kano ya bayyana matakin daya dace Musulmai su dauka

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II yayi kira ga kafatanin al’ummar Musulmai dasu jajirce wajen gudanar da addui’o’i a wannan wata mai alfarma na watan Azumin Ramadana domin kawo karshen matsalar tsaro a yankin Arewacin Najeriya.

Sarki Sunusi ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu a yayin taron daura auren mata 70 da gwamnatin jahar Kano ta dauki nauyinsu, inda yace ya kamata Musulmai su dage wajen yin addu’o’i ko Allah zai dubemu da idon rahama.

KU KARANTA: Wata sabuwa: An dakatar da sana’ar Acaba a wasu manyan jahohin Arewa guda 5

“Muyi amfani da wannan dama ta Azumin Ramadana wajen gudanar da addu’o’i ta yadda Allah zai dubemu da idon rahama ya kawo mana karshen matsalolin tsaron da suka dabaibayemu.

“Muna fuskantar dimbin matsaloli da dama, musamman satar mutane, talauci, rashin aikin yi, satar shanu da kuma ayyukan yan bindiga, don haka wannan dam ace kyakkyawa da muka samu na watan Ramadana don neman taimako daga Allah.” Inji shi.

Haka zalika Sarki yace akwai bukatar a hada karfi da karfe wajen cimma wannan manufa, inda ya kara da cewa tun daga Malamai, attjirai da gwamnati, dukkaninsu suna da rawar da zasu taka wajen cimma wannan bukata.

A cewar Sarki, akwai bukatar Gwamnati ta bullo da tsare tsare da zasu kawar da talauci a tsakanin al’umma, ta hanyar samar da ayyuka ga matasa, yayin da Malamai zasu cigaba da ilimantar da mabiyansu akan kyawawan tarbiyya, su kuma attajirai su taimaka ma gajiyayyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel