Bana Buhari ba zai yi jinkiri kafin ya nada Ministoci ba – Femi Adesina

Bana Buhari ba zai yi jinkiri kafin ya nada Ministoci ba – Femi Adesina

Mai taimakawa shugaban kasa Muhammadi Buhari da shawara a kan harkokin sadarwa da yada labarai watau Femi Adesina, ya fito ya fadawa ‘Yan Najeriya cewa za a nada Ministoci ba tare da bata lokaci ba a wannan karo.

Femi Adesina ya tabbatar da cewa shugaban kasa ba zai yi wani jinkiri na nada sababbin Ministocin da zai yi aiki da su a wa’adin sa na biyu ba. A wa’adin sa na farko, Buhari ya dauki watanni shida bai kafa gwamnati ba.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya bayyana wannan ne a lokacin da yake hira da Jaridar The Guardian a Ranar Lahadi 6 ga Watan Mayu. Adesina yake cewa Buhari ba zai sake tsayawa wani bata-lokaci wannan karo ba.

Hadimin shugaban kasar ya nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta sa baki wajen nadin Ministocin da za ayi. Adesina yake cewa an umarci Ministoci su bada rahoton aikin da su kayi, wanda wannan zai taimakawa sabon gwamnati.

KU KARANTA: Buhari yace ba zai fadi wadanda zai ba Minista ba

Bana Buhari ba zai yi jinkiri kafin ya nada Ministoci ba – Femi Adesina

Ba za a dauki dogon lokaci wajen nadin Ministoci a 2019 ba
Source: Twitter

Babban mai ba shugaban kasan shawara yake cewa akwai kwamitoci da-dama da ke aiki a game da kafa sabon gwamnatin da za ayi a Ranar 29 ga Watan Mayu. Wannan akasin abin da aka samu ne a 2015, lokacin APC na neman karbar mulki.

Adesina yake cewa daga cikin matsalolin da aka samu a 2015, shi ne irin barnar da aka yi wa tattalin arzikin kasa. Hadimin yake cewa APC za ta tsoma-bakin ta wajen rabon kujerun Ministoci amma sai yadda Buhari ya ga dama za a yi.

A karshe Femi Adesina ya musanya batun cewa wasu Ministocin ba su tabuka komai ba, don haka shugaba Buhari zai yi waje da su. Adesina yake cewa Ministocin sun yi bakin kokarinsu, don haka ne har yau su ke kan kujerun su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel