Buhari yayi jawabin farko yayinda ya isa Abuja daga Landan

Buhari yayi jawabin farko yayinda ya isa Abuja daga Landan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, ya dawo gida Najeriya bayan shafe kwanaki 10 a kasar Birtaniya. Shugaban kasar ya ki cewa komai akan batun sake mambobin majalisarsa.

Bayan dawowarsa shugaba Buhari ya zanta da manema labarai da suka so jin ta bakinsa akan yawan garkuwa da mutane, fashi da makami, yan bindiga da harin ta’addanci a kasar.

Sai dai, a lokacin da ya tsaya domin basu amsar wasu daga cikin tambayoyinsu, musamman wadanda suka nuna damuwa kan kafa sabuwar majalisarsa, Buhari yace, “Ba zan fada maku ba.”

Sai dai kuma, bayan yaki amsa sauran tambayoyin, an nemi ya amsa tambaya kan yawan sace-sacen mutane a kasar, amma sai yace “na lura mukaddashin sufeto janar na yan sanda, Mohammed Adamu ya rairaye, koda dai wannan alamu ne nacewa yana aiki sosai."

Buhari yayi jawabin farko yayinda ya isa Abuja daga Landan

Buhari yayi jawabin farko yayinda ya isa Abuja daga Landan
Source: Depositphotos

Shugaba Buhari ya samu tarba daga shugaban ma’aikatansa, Abba Kyari, ministan birnin tarayya, Muhammed Bello; shugaban hafsan soji, Tukur Buratai, mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Magu da wasu hadimansa.

KU KARANTA KUMA: Kwamishinan yan sandan Katsina ya koma Daura kan sace Magajin Gari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Fadar shugaban kasa ta bukaci 'yan adawa da masu hamayya da gwamnatin tarayya da su janye kalamansu da suka yaudari wasu 'yan Najeriya da shi a kan cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar Ingila ne domin a duba lafiyar sa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan wata ziyara ta 'kashin kan sa' da ya kai zuwa kasar Ingila.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel