Kwamishinan yan sandan Katsina ya koma Daura kan sace Magajin Gari

Kwamishinan yan sandan Katsina ya koma Daura kan sace Magajin Gari

- Kwamishinan yan sandan Katsina, Sanusi Buba ya bar ofishinsa na babbar birnin jihar zuwa Daura

- Hakan ya biyo bayan ci gaba da bincike da aikin ceto Magajin Garin Daura, Musa Umar Uba da yan sandan ke yi

- Masu garkuwa da mutane ne dai suka sace magajin Garin Daura a gidansa

Kwamishinan yan sandan Katsina, Sanusi Buba ya koma Daura, yayinda yan sanda ke ci gaba da bincike da aikin ceto Magajin Garin Daura, Musa Umar Uba.

Majiyoyi sun ce iyalan basaraken da masarautar Daura baki daya sun shiga alhini kan ainahin dalilin sace sa da kuma lafiyarsa.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa CP Buba na a Daura domin ya jagoranci duk wani bincike da aikin ceto da jami’an yan sanda zasu yi don gano wadanda suka yi garkuwa da basaraken sannan su tabbbatar da ceton shi.

Kwamishinan yan sandan Katsina ya koma Daura kan sace Magajin Gari

Kwamishinan yan sandan Katsina ya koma Daura kan sace Magajin Gari
Source: UGC

Da aka tuntube shi a jiya Lahadi, kakakin yan sandan, DCP Frank Mba, ya tabbatar da cewar CP Buba ya bar ofishinsa daga Babbar birnin jihar zuwa Daura, inda yake jagorantar tsaro da aikin bincike don ceto Wanda aka sace a Daura kwanan nan.

KU KARANTA KUMA: Dawowar buhari: Fadar shugaban kasa ta gwasale 'yan adawa da kafafen yada labarai

Haka zalika kakakin yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, yace akwai ci gaba sosai, amma saboda dalilai na tsaro ba zamu bayyana ba a yanzu.

A cewarsa, “muna jiran lokacin da ya dace mu bayyana, amma nasara tamu ce, muna a Daura yanzu haka tare da CP,” inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel