Mayakan Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannu a wata gwabzawa da suka yi da Sojoji

Mayakan Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannu a wata gwabzawa da suka yi da Sojoji

Zaratan dakarun rundunar Sojan Najeriya ta kasa sun samu wata gagarumar galaba akan mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a yayin wata karanbatta da suka yi da juna a ranar Juma’a, 3 ga watan Mayu a jahar Borno.

Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Sojan kasa, Kanal Sagir Musa ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu, inda yace runduna ta 3 na Operation Lafiya Dole dake garin Magumeri ta karkashe mayakan Boko Haram yayin da suka yi kokarin kutsa kai cikin garin Magumeri don neman abinci.

KU KARANTA: Atiku ya haramta naira dubu goma goma da Buhari ke rabawa na Trader Moni

“A yayin wannan dauki ba dadi, Sojojin Najeriya sun karkashe mayakan Boko Haram da dama, tare da jikkata wasu da dama da suka tsere da rauni, kuma a yanzu haka Sojoji na cigaba da bin sawun wadanda suka tsere don gama musu aiki.

“Sai dai a wani hannun an samu Sojoji guda biyar da suka rigamu gidan gaskiya, amma duk da haka Sojojin na cigaba da ankara da duk wani yunkuri na yan ta’adda na yan ta’addan dake kokarin neman abinci” Inji Sagir.

Idan za’a tuna a watan Feburairun daya gabata ne aka kaddamar da rundunar Sojojin hadaka na kasashen dake makwabtaka da Najeriya da suka hada da Chadi, Kamaru, da Nijar don yakar Boko Haram, mai taken ‘Operation Yancin Tafki’.

Wannan aiki yayi matukar tasiri sakamakon ya hana ma mayakan kungiyar ta’addancin walwala da kuma zirga zirga ba kamar yadda suka saba a baya ba, don haka an yanke musu duk wasu hanyoyin da suke bi don samun abinci, ruwan sha, man fetir da sauran bukatu da yau da kullum.]

Daga karshe babban kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Olufemi Akinjobi yay aba da jarumtar Sojojin runduna ta uku a madadin babnban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, sa’annan ya shawarcesu dasu cigaba da jajircewa har sai sun gama da Boko Haram.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel