Mayakan Boko Haram sun sace Fasto da matashi dan bautar kasa a Borno

Mayakan Boko Haram sun sace Fasto da matashi dan bautar kasa a Borno

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun sace wani matashi dan bautar kasa, Abraham Amuta, tare da wani Fasto a cocin 'Living Faith (Winners Chapel)' mai suna Ayeleke a jihar Borno.

Abokan matashin sun bayyana cewar an sace mutanen biyu yayin da suke kan hanyar su ta zuwa Chibok domin raba kayan tallafi ga 'yan sansanin gudun hijira (IDP) tare da yi musu wa'azin da'awar Kiristanci.

Sun ce an kai wa motar dake dauke da su tare da ragowar fasinjoji hari a hanyar zuwa garin Chibok daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

An gano cewar Amuta shine kadai da a wurin iyayen sa.

Mayakan Boko Haram sun sace Fasto da matashi dan bautar kasa a Borno
Matasa 'yan bautar kasa
Source: Depositphotos

Daya daga cikin abokan matashin mai suna Success Ezenwa ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewar, "Abraham Amuta dan bautar kasa ne da aka tura Maiduguri. 'Yan Boko Haram sun sace shi sati biyu da suka wuce. Sun sace shi ne tare da Faston cocinsa a hanyar su ta zuwa gabatar da wa'azin Kirista. Shi kadai ne da a wurin iyayensa. Mu saka shi a cikin addu'a."

DUBA WANNAN: Nadin sabbin ministoci da hadimai: Amsar da Buhari ya bawa manema labarai

"Dan rukuni na 1 ne a ajin 'B" na 'yan bautar kasa da aka tura Maiduguri, jihar Borno. Fiye da sati biyu kenan da sace shi. Wasu mutane dake ikirarin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun dauki alhakin sace shi. Ku taimaka wajen yada wannan sako har ya kai kunnen gwamnatin tarayya."

Saboda yanayin tsaro a jihar Borno, ana bawa 'yan bautar kasa da aka tura zabin su canja zuwa jihar da suke so.

A watan Nuwamba na shekarar 2018 kadai, 'yan bautar kasa 818 daga cikin 1,118 ne a rukunin 'C' suka bar jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel