Nadin sabbin ministoci da hadimai: Amsar da Buhari ya bawa manema labarai

Nadin sabbin ministoci da hadimai: Amsar da Buhari ya bawa manema labarai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai yi magana a kan irin mutanen da zai nada a mukaman siyasa a gwamnatinsa ta gaba ba.

Da yake amsa tambayar manema labarai jim kadan bayan dawowar sa daga kasar Ingila a filin jirage na Nnamdi Azikiwe dake Abuja, Buhari ya bayyana cewar a shirye ya ke domin nada sabon kunshin jama'ar da zu taya shi aiki a zangonsa na biy.

Wani dan jarida ya tambayi shugaba Buhari, "wanne irin mutane za ka bawa mukami a gwamnatin ka wannan karon?", sai ya bashi amsa da cewar, "ba zan fada maka ba."

A yau ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan wata ziyara ta 'kashin kan sa' da ya kai zuwa kasar Ingila.

Nadin sabbin ministoci da hadimai: Amsar da Buhari ya bawa manema labarai
Buhari, bayan dawowar sa daga kasar Ingila
Source: Twitter

Jirgin shugaba Buhari ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake babban birnin tarayya da misalin karfe 6:24 na yamma.

DUBA WANNAN: Kididdiga: Shugaba Buhari ya shafe kwanaki 227 a ziyara 9 da ya kai kasar Ingila a shekara 4

A wani jawabi da kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar, ya gwasale wasu kafafen watsa labarai da mambobin jam'iyyar adawa da wasu kungiyoyin adawa a kan kwarmata cewar shugaba Buhari ya tafi kasar Ingila ne saboda bashi da lafiya, a saboda haka ba zai dawo bayan kwana 10 da ya ambata ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel