Da duminsa: An ga wata

Da duminsa: An ga wata

Kwamitin ganin wata (NMSC) ya sanar da cewar mai alfarma sarkin Musulmi, Abubakar Saad II, ya umarce shi ya sanar da al'ummar Musulmi cewar an ga watan Ramadana da yammacin yau a wurare daban-daban dake fadin kasar nan.

Kwamitin ya ce za a iya fara sallar Taraweeh, tare da bayyana cewar sarkin Musulmi, wanda kuma shine shugaban kwamitin ganin wata, zai bayar da sanarwa nan ba da dadewa ba.

Sakataren kwamitin koli na harkokin addinin Musulunci a Najeriya, Ishaq Oloyede, ne ya shaida wa manema labarai hakan.

Da duminsa: An ga wata

Sarkin Musulmi; Saad Abubakar III
Source: Twitter

Ganin jaririn watan ya tabbatar da cewar Musulmi a ko ina cikin fadin duniya za su tashi da azumi a bakin su ranar Litinin.

Lokacin azumin watan Ramadana, Musulmi na kame bakin su daga ci da sha daga hudowar alfijir zuwa faduwar rana har sai an ga wani sabon watan.

DUBA WANNAN: Auren zawarawa: Ganduje ya biya miliyan N30 a matsayin kudin sadakin amare 1500

Da yake sanar da ganin watan a fadar sa, sarkin Musulmi ya ce kwamitin duban wata ya tabbatar da ganin sabon watan Ramadana a birane da dama da ke kasar nan.

Ya umarci al'ummar Musulmi su tashi da azumi ranar Litinin. Kazalika, ya yi kira gare su da su yi amfani da albarkar da ke cikin watan wajen yiwa Najeriya da shugabanninta addu'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel