'Yan bindiga sun yi garkuwa da sakatariyar dindindin ta gwamnatin jihar Taraba

'Yan bindiga sun yi garkuwa da sakatariyar dindindin ta gwamnatin jihar Taraba

Da sanadin rahotanni na jaridar The Punch mun samu cewa, wasu 'yan bindiga a ranar Lahadin da ta gabata, sun tasa keyar sakatariyar dindindin ta ma'aikatar ruwa a gwamnatin jihar Taraba, Susana Jonathan.

Misis Susana ta fada hannun masu garkuwa da mutane da misalin karfe 2.17 na daren ranar Lahadi a gidan ta da ke yankin ATC cikin birnin Jalingo kamar yadda makwabta su ka bayar da shaida.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da sakatariyar dindindin ta gwamnatin jihar Taraba

'Yan bindiga sun yi garkuwa da sakatariyar dindindin ta gwamnatin jihar Taraba
Source: UGC

Wannan lamari ya auku kwanaki biyar bayan fadawar wani babban ma'aikacin jami'ar jihar Taraba cikin tarkon masu garkuwa da mutane, Mista Sanusi Sa'ad, wanda gidan sa ke makotaka da na Sakatariya Susana.

Mashaida wannan mugun ji da mugun gani sun bayar da rahoton cewa, masu ta'adar sun ribaci makami na bindigu wajen razanar da al'umma yayin cin karen su babu babbaka na dauke Sakatariya Susana daga mahallin ta.

KARANTA KUMA: Watan Azumin Ramalana ya bayyana a Najeriya - Sarkin Musulmi

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, DSP David Misal, ya bayar da shaidar sa ta aukuwar wannan mummunan lamari yayin ganawar sa da manema labarai a birnin Jalingo.

Makonni biyu da suka gabata masu garkuwa da Mutane sun yi awon gaba da wasu Mata biyu masu dakin Sakataren dindindin na ofishin mataimakin gwamnan jihar Taraba, Haruna Manu. An yi sa'a ta sakin su bayan biyan kudin fansa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel