Buhari ya dawo Najeriya

Buhari ya dawo Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan wata ziyara ta 'kashin kan sa' da ya kai zuwa kasar Ingila.

Jirgin shugaba Buhari ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake babban birnin tarayya da misalin karfe 6:24 na yamma.

A wani jawabi da kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar, ya gwasale wasu kafafen watsa labarai da mambobin jam'iyyar adawa da wasu kungiyoyin adawa a kan kwarmata cewar shugaba Buhari ya tafi kasar Ingila ne saboda bashi da lafiya, a saboda haka ba zai dawo bayan kwana 10 da ya ambata ba.

Buhari ya dawo Najeriya

Saukowar Buhari daga jirgi
Source: Twitter

Buhari ya dawo Najeriya

Buhari na gaisa wa da Femi Adesina
Source: Twitter

Buhari ya dawo Najeriya

Buhari ya dawo Najeriya
Source: Twitter

A cewar Adesina, "a muguwar aniya irin ta wadannan mutane, sun yada labarin kanzon kurege a kan cewar wasu likitoci sun shawarci shugaba Buhari ya kara zama a kasar Ingila saboda tsanantar halin rashin lafiya."

DUBA WANNAN: Azumi: Ta tabbata, an ga wata Ramadana

Ya kara da cewa: "to yanzu da shugaba Buhari ya dawo, ko irin wadannan mutane za su janye kalaman su? ko zasu fito su nemi afuwar 'yan Najeriya a kan labarin karyar da suka yada?"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel