Ina tunkaho da cewa Jam’iyyar PDP ce ta kawo ‘Yaradua – Atiku

Ina tunkaho da cewa Jam’iyyar PDP ce ta kawo ‘Yaradua – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, yayi magana a yau 5 ga Watan Mayu 2010 domin tunawa da Marigayi shugaban kasa Ummaru ‘Yaradua da ya rasu a irin wannan rana.

Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa mai matukar alfahari da cewa jam’iyyarsa ta PDP ce ta fito da Marigayi Ummaru Musa ‘Yaradua. Shugaba ‘Yaradua ya rasu ne Ranar 5 ga Watan Mayun 2010 lokacin yana kan mulki.

Atiku Abubakar yake bayyana shugaba Ummaru ‘Yaradua da shugaba kuma mutumin kirki. Atiku yace Marigayin ya kasance mai hangen nesa wanda ya kawo zaman lafiya a yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur a Najeriya.

‘Yaradua yayi kokarin ganin wanzuwar zaman lafiya a Neja-Delta inda ake fama da rikici bayan ya kawo wani tsari na yi wa Tsageru afuwa. Atiku ya kara da cewa ya shaku da tsohon shugaban kasar a siyasa a lokacin yana raye.

KU KARANTA: Manyan Kasa sun tuna da Marigayi Shugaba 'Yaradua

Ina tunkaho da cewa Jam’iyyar PDP ce ta kawo ‘Yaradua – Atiku

Atiku Abubakar ya shiga cikin masu makokin ‘Yaradua
Source: UGC

Atiku yake cewa da shi da Ummaru ‘Yaradua duk sun koyi karatun siyasa ne a wajen Maigidan sa Marigayi Janar Shehu Musa Yar’Adua. Atiku yace tsohon Sojan ne ya koya masu yadda ake wanke allon siyasa tun a shekarun baya.

Bayan haka kuma, ‘dan takarar shugaban kasar na PDP a zaben bana yace yayi aiki da Ummaru ‘Yaradua sosai a lokacin yana mataimakin shugaban kasa, a wancan lokaci shi kuma Marigayi Ummaru ‘Yar’adua yana gwamnan Katsina.

‘Dan siyasar ya bayyana irin nasarorin da ‘Yaradua ya samu a lokacin yana mulki, musamman a bangaren tattalin arziki da harkar mai. A karshe, Atiku yace ‘Yaradua ya san tsarin mulki, yana mai masa addu’ar samun gidan Aljanna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel