Watan Azumi: Kayan masarufi sun tashi a jihar Legas

Watan Azumi: Kayan masarufi sun tashi a jihar Legas

Yayin da Musulmai ke gab da shiga watan Azumin Ramalana a fadin duniya, farashin kayan gwari irin su Tumatur da attaruhu, sun yi tashin doron zabuwa da kimanin kaso sittin cikin dari na farashin su a jihar Legas.

Binciken kamfanin dillancin labarai na kasa cikin kasuwannin Mil 12, Oke Odo, Oyingbo da Iddo da ke jihar Legas, ya tabbatar da cewa farashin kwando guda na tumatir da ake sayarwa N5000 makonni biyu da suka gabata ya tashi zuwa N12,000.

Watan Azumi: Kayan masarufi sun tashi a jihar Legas

Watan Azumi: Kayan masarufi sun tashi a jihar Legas
Source: Original

Kazalika farashin kwando guda na tattasai da aka saba sayarwa a kan N6,000 ya tashi zuwa N12,000. Farashin attaruhu da farashin sa makonni biyu ya ke a kan N5,000, ya koma zuwa N9,000 kamar yadda binciken ya tabbatar.

Wani jagoran kungiyar masu sayar da kayan gwari a kasuwar Mil 12, Haruna Muhammad, ya alakanta bazara da kuma tsadar sufuri da hauhawar farashin kayan miya. Sai dai ya ce duk wannan tsada an samu saukin farashin kayan masarufi idan an kwatanta da farashin su shekaru biyu da suka gabata.

A sabanin haka, an samu sauki na farashin wasu kayan masarufi irin su Albasa, Man ja da kuma Man gyada kamar yadda wani mai sayar da wake a kasuwar Iddo, Musa Yahaya ya bayar da shaida.

KARANTA KUMA: Jonathan, Atiku da Saraki sun yi alhinin tunawa da mutuwar tsohon shugaban kasa 'Yar adu'a

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, Sarkin Musulmi Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad, ya nemi daukacin al'ummar Musulmi na Najeriya da su sanya idanun lura wajen laluben sabon watan Ramalana na shekarar 1445.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel