Gwamna Ganduje Yace Zai Ma Hukumar Hizbah Gyaran Fuska

Gwamna Ganduje Yace Zai Ma Hukumar Hizbah Gyaran Fuska

- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje yace Hukumar Hizba ko ‘Yansandan Shari’a na karkacewa daga turbar da aka dora ta akai kuma tana bukatar ayi mata garambawul.

- Shugabannin Hizbar saboda rashin sani suna ganin cewa yin mabanci ga mutane abu ne da ya dace a yi.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje yace Hukumar Hizba ko ‘Yansandan Shari’a na karkacewa daga turbar da aka dora ta akai kuma tana bukatar ayi mata garambawul.

“Gwamnati ba za ta kara amincewa da irin ayukkan da ba su dace ba da shugabannin Hizbah ke aikatawa” In ji gwamna.

KU KARANTA: Afirka ta Kudu: ’Yan fashi sun daba ma dan Najeriya wuka har ya mutu Read more:

“Shugabannin Hukumar da ake sa ran su yi amfani da koyarwar Alkur’ani da Hadisin Manzon Allah (SAW) amma suna bin ra’ayoyin wasu mutane.

Yace “kuma abun takaici shine, shugabannin Hizbar saboda rashin sani suna ganin cewa yin mabanci ga mutane abu ne da ya dace a yi. Ba za a yarda da wannan ba, kuma gwamnati za ta magance wannan matsalar.”

Gwamnati da masarautar Kano da al’umma baki daya suna da irin rawar da za su taka. Kuma a matsayin Hizbah na Hukumar da aka kafa don gyaran halin al’umma tana da babbar rawar da za ta taka wurin tabbar da cikakken aiki da doka.”

Gwamna Ganduje yace za a yi ma Hukumar Hizbah garambawul don ta taimaka wurin kaddamar da Dokar Iyali.

Mai martaba Sarkin Kano Sanusi na II, wanda ya kawo Dokar Iyali ta Jihar Kano yace dokar za ta yi aiki ne kan kalubalen da suka shafi sha’anin aure a jihar Kano kawai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu. Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel