Ka fita wajen APC ka zakulo Ministocin ka – An fadawa Buhari

Ka fita wajen APC ka zakulo Ministocin ka – An fadawa Buhari

Wasu Bayin Allah a Najeriya sun fito sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya zakulo wasu daga cikin Ministocinsa wannan karo daga wajen jam’iyyar sa ta APC mai mulkin kasar.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Punch, wasu ‘yan gwagwarmaya da masana a kasar nan ne su kayi wannan kira ga shugaban kasa Buhari, a daidai lokacin da ake shirin kafa sabuwar gwamnati mai-ci a kusan fadin Najeriya.

Moshood Erubami, wanda shi ne shugaban kungiyar ‘Nigeria Voters Assembly’, ya nemi shugaba Buhari ya zabo wasu daga cikin wadanda yayi takarar kujerar shugaban kasa da su a zaben 2019, ya ba su ofishin Minista a gwamnatinsa.

KU KARANTA: An hana kowa ganin Shugaban kasa a kan batun raba Ministoci

Ka fita wajen APC ka zakulo Ministocin ka – An fadawa Buhari

Ana so Buhari ya tafi da irin su Oby Ezekwesili a Gwamnatinsa
Source: Facebook

Erubami yake cewa akwai ‘Yan takarar da bai kamata Buhari yayi watsi da su ba domin zai ga aiki da cikawa idan ya ba su mukami. Daga cikin wadanda ake rokon a ba mukami akwai Oby Ezekwesili, Kingsley Moghalu da Yele Sowore.

Wani Malamin harkar siyasa a wata jami’a a Jihar Ogun, Femi Otunbajo, ya bayyana cewa duk da abu ne mai kyau shugaba Buhari ya zakulo Ministocinsa daga wajen APC, sai dai zai yi wahala ‘Yan PDP su karbi tayin Minista daga Buhari.

Farfesa Femi Otunbajo, yake cewa ganin yadda Abokin hamayya, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya shigar da kara a kotu yana ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben bana, zai yi wa manyan ‘Yan adawa su yarda su yi aiki a gwamnatin APC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel